Masu shan fetur da POS za su rika biyan karin N50 daga Disamba – IPMAN

Masu shan fetur da POS za su rika biyan karin N50 daga Disamba – IPMAN

Jaridar Daily Trust ta rahoto kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwan mai a Najeriya, ta na sanar da jama’a cewa daga Ranar 1 ga Watan Disamban 2019, za a sa karin N50 a kowace tashar PoS.

Gidajen mai za su sa wannan kari ne ga wadanda za su saye man akalla N1, 000 kamar yadda kungiyar IPMAN wanda ‘ya ‘yanta su ka mallaki gidajen mai ta bayyana mana a farkon makon nan.

Kungiyar ta ce an kawo wannan doka ne bisa wani sabon umarni da babban bankin Najeriya na CBN ta yi. Gwamnan CBN ya bada umarnin sa haraji ne ga cinikayyar da ake yi da na’urorin zamani.

A cewar IPMN, Ranar 17 ga Satumba su ka samu takarda daga CBN inda aka bukaci bankuna su sa wannan haraji. A dalilin wannan ne bankuna za su cire wannan kudi a hannun gidajen man kasar.

KU KARANTA:Shugaba Buhari ya yi watsi da bukatun Ministan shari'a

Wannan kungiya ta jawo hankalin jama’a cewa kudin da za a rike zaftarewa za su shiga hannun banki ne ba wajensu ba. Jawabin ya ce: “IPMAN ba ta cikin wadanda za su ci moriyar wannan tsari.”

Inda za a samu matsala kuma shi ne, shugaban kungiyar IPMAN ta kasa baki daya, Chinedu Okoronkwo, ya shaidawa ‘Yan jaridar Daily Trust cewa sam bai da labarin wannan bayani gaba daya.

Mista Chinedu Okoronkwo ya ce bai sa hannu a kan wannan sanarwa ba. “Ba gaskiya ba ne. Babu adireshi a sanarwar, kuma ba a sa hannu ba.” Inji sa. Wannan ya sa ya ce watakila aikin ‘yan damfara ne.

Sai dai babu shakka babban bankin Najeriya, CBN, ya umarci duk wasu bankuna su rika karbar N50 a matsayin ladan aikin amfani da manhajar PoS. CBN sun bada wannan umarni ne a Watan Satumba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel