Magani a gonar yaro: Amfani guda 11 da gwaza da ganyenta suke yi a jikin dan adam

Magani a gonar yaro: Amfani guda 11 da gwaza da ganyenta suke yi a jikin dan adam

- Masana kiwon lafiya sun bukaci jama’a da su yawaita cin ganyen gwaza

- Yana dauke da sinadarai masu matukar amfani ga jikin dan Adam tare da bada kariya

- Ana iya sarrafa ganyen gwaza kamar sauran abinci ta hanyar dafa shi ko miya da ganyen

Masana kiwon lafiya sun bukaci jama’a da su yawaita cin ganyen gwaza. A cewarsu, yana dauke da sinadarai masu amfani ga jikin dan Adam.

Bincike ya nuna cewa, ganyen gwaza na dauke da sinadarin kawar da cututtuka da suka hada da makanta, daji, hawan jini da sauransu.

Ana iya sarrafa ganyen gwaza kamar sauran abinci ta hanyar dafa shi ko kuma miya da ganyen. A yankin arewacin Najeriya kuwa, ana dafa ganyen gwaza domin cin shi a haka, ko da manja ko man gyada ko kuma da miya. Ga kadan daga cikin amfanin gwaza a jikin dan Adam.

KU KARANTA: Allah ya shirya mana zuri'a: An kama saurayi da budurwa suna lalata a cikin aji

1. Ganyen gwaza na kare mutum daga kamuwa da cututtuka saboda sinadarin ‘Vitamin C’ da yake dashi.

2. Yana ba wa mutum kariya daga kamuwa da cutar daji kowacce iri.

3. Gwaza na kare dan Adam daga kamuwa da cutar sigari.

4. Yana kara karfin jijiyoyin jiki har da mazakuta.

5. yana taimakawa wajen nika abinci, kawar da ciwon ciki da hana yawan bahaya.

6. Yana dauke da sinadarin ‘Calcium’ wanda ke kara karfin kashi da hakora.

7. Ganyen gwaza na kare mutum daga kamuwa da hawan jini.

8. Yana dauke da sinadarin ‘Folate’ wanda ke inganta girman dan ciki.

9. Gwaza na inganta maniyyi a jikin maza.

10. Yana kara jini a jikin mutum musamman ga yara kanana.

11. Tana maganin yunwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng