Allah ya shirya mana zuri'a: An kama saurayi da budurwa suna lalata a cikin aji

Allah ya shirya mana zuri'a: An kama saurayi da budurwa suna lalata a cikin aji

- Matsalar lalata tsakanin daliban manyan makarantun gaba da sakandire ta zama ruwan dare

- Cikin kwanakin nan ne jami’ar Babcock ta kori wata daliba a kan bidiyon da ake lalata da ita ya bayyana

- Folitaknik din jihar Edo ma ta fatattaki dalibai biyu a kan kamasu da aka yi suna lalata a dakin karatu

Matsalar latata tsakanin daliban manyan makarantun gaba da sakandare ya addabi manyan makarantun kasar nan a 'yan kwanakin nan. Wanda aka yi ba da dadewa ba kuwa shine na jami’ar Babcock, wanda aka gano bidiyon wata budurwa suna lalata da saurayi.

Babu jimawa kuwa, hukumar jami’ar ta fatattaki dalibar. Hakan kuwa ya jawo cece-kuce daga wajen mutane da dama. Wasu na ganin anyi dai-dai da aka kori dalibar inda wasu ke ganin akasin hakan.

Wasu na kafa hujjar cewa, lamarin bai faru a cikin makarantar ba, don haka hukumar makarantar bata da hurumin katsalandan ga rayuwar dalibar.

Amma sai dai kash! Sun manta cewa, shaidar digirin ana bada ita ne saboda kyakkyawar dabi’a da kuma ilimi. Duk inda aka rasa dabi’a ta gari, toh kuwa ilimin na iya samun babbar nakasa.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: An kori daliban wata sakandare 71 bayan sun shiga kungiyar asiri

Kwatsam kuma sai labarin wasu dalibai biyu da folitaknik din jihar Edo ta kora ya mamaye kanun labarai. Su kuwa daliban an koresu daga makarantar ne sakamakon kamasu da aka yi suna lalata a cikin dakin karatu.

Takardar da makarantar ta fitar da ke bayyana korar daliban, ta nuna cewa an kamasu dumu-dumu a dakin karatu suna aikata badalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel