Innalillahi: Daga zuwa gidan biki yaro ya tsunduma cikin tukunyar girkin abincin biki

Innalillahi: Daga zuwa gidan biki yaro ya tsunduma cikin tukunyar girkin abincin biki

- Wani yaro mai shekaru hudu ya tsunduma tukunyar biki yayin da take kan wuta

- Lamarin ya faru ne a birnin Shabad a cikin jihar Telangana ta kasar India

- Bayan kwana daya da aukuwar lamarin, yaron ya rasa ranshi sakamakon muguwar kunar da ya samu

Wani yaro mai shekaru hudu ya fada tukunyar abincin biki inda daga baya ya rigamu gidan gaskiya, kamar yadda hukumar ‘yan sandan India suka bayyana.

Hukumar ‘yan sandan ta ruwaito cewa, hatsarin ya faru ne a ranar Litinin bayan da yaron ya ke wasa kusa da tukunyar, yayin da take dore a kan wuta.

An gano cewa, iyayen karamin yaron ‘yan asalin birnin Shabad ne da ke jihar Telangana. Suna biki ne a gidansu wanda hakan ne ya yi sakamakon faruwar mummunan lamarin.

Tuni aka kwashi yaron da ya babbake zuwa asibiti. Kamar yadda hukumar ‘yan sandan ta sanar, yaron ya mutu ne bayan kwana daya da kaishi asibitin. Ya rasa ranshi ne sakamakon mummunar kunar da ya yi.

‘Yan sandan sun ce, suna binciken lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar karamin yaron.

KU KARANTA: 'Ya'yana guda 70 ne suka haddace Al-Qur'ani mai girma daga Baraka har Nasi - Sheikh Dahiru Bauchi

Ba wannan ne karo na farko ba da yara kanana suka fara rasa rayukansu, sakamakon ganganci ko rashin kular iyayensu.

A nan Najeriya, akan samu yara kanana da kan fada rijiya ba tare da sanin iyayen ba. Kananan yaran kan rasu ko kuma su jigata, sakamakon shan ruwan da suka yi bayan fadawa rijiyar.

Yana da kyau mutum ya sa ido tare da ba wa yara kanana da basu san ciwon kansu ba kula mai tsanani. Daga kan abinda zasu saka a bakinsu zuwa inda zasu saka kafafunsu ko abinda zasu yi wasa dashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel