Ikko ikon Allah: Yansanda 1000 sun dira jahar Legas don warware cushewar motoci a kan tituna

Ikko ikon Allah: Yansanda 1000 sun dira jahar Legas don warware cushewar motoci a kan tituna

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas ta aika da karin jami’anta guda 1000 zuwa jahar Legas domin su warware matsalar cunkoson ababen hawa da ake samu a yawancin titunan dake cikin birnin jahar.

Idan za’a tuna wannan matsala ta cushewar ababebn hawa a kan tituna ta dade tana ci ma al’ummar da gwamnatin jahar Legas tuwo a kwarya, wanda hakan ke sanya jama’a kwashe tsawon awanni kikam a tsakiyar titi ba tare da sun motsa ba.

KU KARANTA: Yan bindigan dake fitinar jahar Zamfara abokanka ne, ka sansu – Yari ga Matawalle

Bugu da kari jahar Legas jaha ce dake dauke da dimbin miliyoyin jama’a daga dukkanin sassan Najeriya, shi yasa ma ake mata kirari da cunkus dakin tsumma, makarinki sai an karya! Har ta kai wasu mutane sun gwammace tafiyan kasa a kan su shiga mota.

Jaridar Aminiya ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar, Hakim Odumosu ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba yayin da yake jawabi a wani taron gaggawa daya gudana a babban ofishin Yansandan jahar inda aka tattauna hanyoyin shawo kan matsalar.

Kwamishina Hakim ya kira wannan taro ne bayan kwanaki biyu da kama aiki a matsayinsa na kwamishinan Yansandan jahar Legas, kuma taron ya samu halartar manya manyan hafsoshin rundunar Yansandan.

A wani labari kuma, babban hafsan sojan kasa, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya gudanar da gyara a tsohuwar makarantar firamarin da ya yi, LEA Unguwar Sarki Kaduna, sa’annan ya baiwa makarantar kyautan littafan karatu guda 1,000.

Buratai ya gudanar da wannan aiki ne ta karkashin gidauniyarsa, watau Tukur and Tukur foundation inda yace a shekarar 1967 ya fara makarantar LEA Unguwar Sarki, kuma ya ga amfanin ilimin daya samu, don haka ya kashe mata makudan kudade.

Ita dai wannan makaranta an samar da ita ne a shekarar 1953 kafin samun yanci, amma a sanadiyyar wannan aikin alheri da Buratai ya gudanar a cikinta, a yanzu tana da; dakin kwamfuta, dakin karatu, ban daki na zamani guda 16, wajen wasan yara da kuma kayan karatu da koyarwa haka zalika ya kara musu azuzuwa 8.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel