Daga tambaya sai cibi ya zama kari: Matashi ya kashe wata mata mai ciki saboda kawai ta tambayeshi ranar da zai yi aure

Daga tambaya sai cibi ya zama kari: Matashi ya kashe wata mata mai ciki saboda kawai ta tambayeshi ranar da zai yi aure

- Wani saurayi mai shekaru 28 a duniya ya kashe wata mai ciki kuma makwabciyarshi har lahira

- Makwabciyar tashi, ta dameshi da tambayar yaushe zai yi aure ne, abinda ke bata ma saurayin rai

- Akwai yuwuwar saurayin ya kare rayuwarshi a gidan yari sakamakon ajalin Asiyah da yayi

A ranar 19 ga watan Janairu 2018, wani saurayi mai shekaru 28 a duniya, ya halaka makwabciyarshi bayan da ta dameshi da tambayar, 'Yaushe za ka yi aure?' Wannan lamarin ya faru ne a Kampung Pasir Jonge, dake kasar Indonesia.

Kamar yadda Astro Awani da Sinar Harian suka ruwaito, saurayin mai suna Faiz Nurdin na zaune a gaban gidanshi ne lokacin da makwabciyarshi mai ciki ta sameshi. Asiya mai shekaru 32 a duniya ta saba tambayar makwabcinta lokacin da zai yi aure.

Wanda ake zargin ya ce, matar ta ce mishi, “kayi maza kayi aure, sauran na ta yin aure, me yasa ka ki yin aure har yanzu?” wadannan kalmomi kuwa sun bata mishi rai.

KU KARANTA: San barka: Ahmed Musa ya dauki nauyin karatun matasa 100 A Jami'ar SkyLine dake Kano

Daga baya ya shiga gidan Asiyah da zummar ziyartarta, inda ta yi mishi iso a falo. Ta juya don shiga dakin barci, kawai sai Faiz ya bi ta a baya tare da turata kan gado. Mai cikin ta yi kokarin kare kanta ta hanyar cizon saurayin amma hakan bai yiwu ba.

Ya tsere tare da barin inda abin ya faru amma jami’an tsaro sun kamashi. A yayin da ya yi niyyar guduwa, bayan sun harbi kafarshi da bindiga.

An gano cewa, wanda ake zargin zai kare rayuwarshi ne a gidan yari.

Idan zamu fadi gaskiya, da yawa daga cikinmu ana musu irin wadannan tambayoyin masu kona zuciya. Tabbas akwai ban haushi, amma kuma baya nufin mu illata masu mana wadannan tambayoyin. Allah ya garfarta wa Asiyah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel