Janar Buratai ya gyara firamarin da ya yi a Kaduna, ya bata kyautan littafai 1000

Janar Buratai ya gyara firamarin da ya yi a Kaduna, ya bata kyautan littafai 1000

Babban hafsan sojan kasa, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya gudanar da gyara a tsohuwar makarantar firamarin da ya yi, LEA Unguwar Sarki Kaduna, sa’annan ya baiwa makarantar kyautan littafan karatu guda 1,000.

Jaridar BluePrint ta ruwaito Buratai ya gudanar da wannan aiki ne ta karkashin gidauniyarsa, watau Tukur and Tukur foundation inda yace a shekarar 1967 ya fara makarantar LEA Unguwar Sarki, kuma ya ga amfanin ilimin daya samu, don haka ya kashe mata makudan kudade.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Alkali ya tausaya ma Maina saboda yana zubar da jini a kotu

Ita dai wannan makaranta an samar da ita ne a shekarar 1953 kafin samun yanci, amma a sanadiyyar wannan aikin alheri da Buratai ya gudanar a cikinta, a yanzu tana da; dakin kwamfuta, dakin karatu, ban daki na zamani guda 16, wajen wasan yara da kuma kayan karatu da koyarwa haka zalika ya kara musu azuzuwa 8.

Babban kwamandan rundunar Sojan kasa ta 1, Manjo Janar Yahaya Faruq ne ya bayyana haka yayin da ya wakilci Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai wajen kaddamar da ayyukan tare da mika littafan 1000 dake kunshe da tarihin Buratai, wanda ake kira ‘Legend of Buratai’.

“Na yi farin cikin halartar wannan makaranta a yau a matsayin wakilin babban mutum kuma abin koyi wanda ya waiwayi makarantarsa kuma ya gyarata, yawancinmu da muke aiki tare dashi bamu yi mamakin hakan ba saboda mun san mutum ne mai son cigaban mutane.

“Shi kansa Buratai makarantar horas da malamai ya yi, don haka halastaccen malami ne wanda ya fahimci muhimmancin ilimi, wannan ya nuna mana dacewar mu waiwayi wadanda suka taimakemu a rayuwa, muma mu taimaka musu.

“A yau ina mika muku kwafin littafai guda 1000 ga malamai da daliban makarantar LEA Unguwar Sarki, ina fata zaku yi amfani dasu wajen neman ilimi.” Inji shi.

A nata jawabin, shugabar makarantar, Hajiya Sa’adatu Umar ta bayyana farin cikinta tare da godiya ga Buratai, sa’annan ta yi alkawarin zasu kula da duk ayyukan da ya yi a makarantar, tare da yin amfani da littafan yadda ya kamata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel