Kwamacala: Saurayi dan shekara 31 ya auri kakarsa mai shekaru 91

Kwamacala: Saurayi dan shekara 31 ya auri kakarsa mai shekaru 91

- Wasu masoya sun bayyanawa duniya cewa shekaru ba komai bane kuma ba zasu zama shinge ga kaunar da suke wa juna ba

- Saurayin mai shekaru 31 ya tsunduma cikin soyayyar wata mata sa’ar kakarshi mai shekaru 91 a duniya

- Sun fara haduwa ne a shekarar 2009 a wani kantin sayar da littafai inda yayi mata tayin soyayyarshi kuma ta yi caraf ta karba

Wadannan masoyan sun nuna cewa, shekaru ba shinge bane a soyayya. Kyle Jones mai shekaru 31 a halin yanzu yana soyayya da Marjorie McCool, tsohuwa mai shekaru 91 wacce zata yi sa’ar kakarshi.

Kamar yadda muka gano kuma jaridu da yawa suka ruwaito, Marjorie na matukar son saurayin nata mai shekarun jikanta. Ta yi bayanin irin romon soyayyar da suke kwasa tare da masoyinnata.

“Gaskiya muna more soyayyarrmu kuma sau da yawa muna hira a waya amma ta masoya. Muna fita shan iska tare inda muke jindadin kasancewa tare da junanmu,”

“Mata da yawa na mamakin me nake so a tare da ita. Layikan wuyanta tare da tattarewar fatar ce ke birgeni. Mata kullum damuwarsu zubewar nononsu, amma ni kuwa nafi son wadanda suka zube din. Ba zan ce furfura ba, amma inason kyallin gashin kanta.” Cewar Kyle.

Masoyan sun fara haduwa ne a wani kantin sayar da littatafi a shekarar 2009. Marjorie ta yi shekaru 37 da rabuwa da mijinta amma daga baya sai ta amince da tayin soyayyar Kyle.

KU KARANTA: Kaduna: Aisha tayi yunkurin yankewa Abdullahi mazakuta bayan yace ba zai aureta ba

Duk da mutane sunyi ta zargin Kyle ko kudinta yake so, Marjorie ta ce bata da kudin ita tun farko.

“Mutane da yawa na min kallon ungulu, ko saboda gado nake sonta, amma sam ni ba haka bane,” Kyle ya yi bayani.

Banda Marjorie da ta ke sa’ar kakar Kyle, saurayin yana soyayya da mata sun kai biyar kuma duk sun girmeshi.

“Da farko ina nuna tsananin kishi na a fili, amma koda yaushe yana bayyyana min nafi sauran. Haka yasa nake sonshi. Ina kokarin saka kayan da zasu ja hankalinshi idan zamu kwanta.” In ji Marjorie.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel