Bidiyo: Wata matsafiya ta rikide ta zama akuya bayan an takurata ta dauki kudin da ta ajiye da gangan dan yara su dauka

Bidiyo: Wata matsafiya ta rikide ta zama akuya bayan an takurata ta dauki kudin da ta ajiye da gangan dan yara su dauka

- Wata mata da ake zargin matsafiya ce ta koma akuya a yankin Oganganmodu da ke jihar Ekiti

- Hakan ta faru ne kuwa bayan da mutane suka tirsasata daukar kudin da ta yadda da gangan

- Ta yadda kudin ne da niyyar yara ‘yan makaranta masu wucewa su dauka, amma sai reshe ya juye da mujiya

Wata mata da ake zargin matsafiya ce ta koma akuya. Hakan ya faru ne kuwa bayan da aka tirsasata daukar kudin da ta yadda da gangan a yankin Oganganmodu na jihar Ekiti.

Kamar yadda rahoto daga jaridar Information Nigeria ya bayyana, matar ta yadda kudin ne da niyyar yara ‘yan makaranta masu wucewa su dauka.

Sai dai kuma kash mutanen yankin sun lura da abinda matar take yi, inda suka tirsasata ta dauki kudin, tana daukar kudin kuwa ta koma akuya.

Ba yanzu aka fara samun irin wadannan abubuwan na faruwa ba. Yanzu dai satar yara ya zama tamkar ruwan dare a kasar nan.

KU KARANTA: Hotuna: Dan sanda ya yiwa direba tsirara ya zane shi saboda ya hana shi cin hanci

Bincike ya bayyana cewa a wancan lokacin masu tsafi da mutanen na yadda kudi, biskit ko alawa da gangan, inda su kuma yaran da basu zata ba ke dauka a matsayin tsintuwa.

A wancan lokacin mutane kan koma doya, dutse, takalmi ko wani abu dai mara rai.

Matsafan kan yi wuf su dauka tare da zargawa karensu igiya, inda zasu je wajen tsafin don aikata aika-aikarsu da mutanen da suka sata.

Ubangiji ya karemu daga miyagun mutane marasa tausayi da Imani, Ameen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel