Allahu Akbar: Anyi rabon gadon dukiyar marigayi Rabilu Musa Ibro

Allahu Akbar: Anyi rabon gadon dukiyar marigayi Rabilu Musa Ibro

- Anyi rabon gadon marigayin jarumin barkwancin nan, Rabilu Musa dan Ibro

- An raba gadon ne bayan da yayi shekaru biyar da kwanta dama sakamakon ciwon hanta da yayi ta fama da shi

- Marigayin ya rasu ya bar mata uku da 'ya'ya 20 a duniya

Kamar yadda tashar tsakar gida ta samo daga jaridar yanar gizo ta Najeriya arewa a ranar Alhamis 1 ga watan Agustan da ya gabata na wannan shekarar, anyi rabon gadon jarumi Rabilu Musa dan Ibro da ya kwanta dama shekaru biyar da suka gabata.

Marigayin dan wasan barkwancin ya bar tsabar kudi a asusun ajiyarsa na bankin Union har naira miliyan 30. Marigayin ya bar motocin tirela biyu da bus guda biyu. Ya mallaki gida daya a Gwarinpa Abuja. Ya mallaki gidajen siyar da man fetur 2, daya a Wudil, dayan kuma a titin Yola a Kaduna. Akwai kuma gidan da yake aikin gininsa ba a kammala ba.

Marigayin ya rasu ne a ranar 9 ga Disambar 2014. Mutuwarsa na daya daga cikin manyan rashi da aka yi wanda ta girgiza masana'antar Kannywood bayan rasuwar marigayi Ahmad S. Nuhu wanda ya rasu yana tsaka da tashensa a masana'antar. Rasuwar kuwa ta jefa mutane da dama cikin alhini da jimami.

KU KARANTA: Amarya ta kone dan kishiyarta saboda tayi mafarki yana saduwa da ita

Kafin marigayin ya kwanta dama, shine shugaban 'yan fim din arewa da harkar camama.

An haifi marigayi dan Ibro ne a garin Dan Lasan dake karamar hukumar Warawa dake Kano. Ya rasa rasu ne sakamakon fama da ciwon hanta da yayi. Ya rasu yana da shekaru 47 a duniya inda ya bar mata 3 da 'ya'ya ashirin.

Allah ya jikan marigayin jarumin barkwancin ya kuma sa aljanna makomarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel