Duk lokacin da muka samu sabani da mijina sai ya yayyaga duk kudin da nake da su - Matar aure ta koka a kotu

Duk lokacin da muka samu sabani da mijina sai ya yayyaga duk kudin da nake da su - Matar aure ta koka a kotu

A ranar juma'a ne wata kotun gargajiya da ke zamanta a Ado-Ekiti ta raba wani aure da aka daura shi shekaru 25 da suka wuce a tsakanin wata mata mai suna Kikelomo da mijinta mai suna Joseph Ogundele.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa kotun ta tsayar da ranar Juma'ar a matsayin ranar da zata yanke hukunci a kan karar bayan kowanne bangare; mai kara da wanda ake kara, ya kammala gabatar da korafinsa da hujjojinsa.

NAN ta rawaito cewa kotun ta raba auren ne saboda saurin fushi, yawan duka, tayar da hankali, da lalata dukiyar Kikelomo da Ogundele ke yawan yi.

Kikelomo, mai shekaru 40 a duniya, ta sanar da kotun cewa ta rabu da mijinta, Ogundele, a shekarar 2017 kafin su sake yin wani auren a shekarar 2018.

Ta ce tana sana'ar sayar da abinci yayin da shi kuma mijinta ke sana'ar kafinta, amma duk da haka babu zaman lafiya a gidansu.

DUBA WANNAN: Mata da miji sun gano cewa ubansu daya bayan shekaru 24 da aure

A cewarta, sau biyu tana siya wa mijinta mota bisa tsammanin cewa aiki da motar zai kawo saukin matsalolin da suke yawan samu.

Kikelomo ta kara da cewa duk kokarinta na tallafa wa mijinta ya samu sana'ar dogaro da kai ya ci tura.

"Na siya masa babura guda uku domin yake kula wa da yadda za a ke neman kudi da su, amma ya siyar da su ba tare da sani ba. Na siya masa fili, amma ya kewaye ya karbe kudin daga baya," a cewarta.

Kazalika, ta sanar da kotun cewa duk lokacin da suka samu sabani da mijinta sai kawai ya shiga daki ya tattara kudin da ta dawo da su daga wurin sana'a ya yayyaga su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel