Yadda wani kabilar 'Igbo' ya sace yarinya bahaushiya tare da dirka mata ciki

Yadda wani kabilar 'Igbo' ya sace yarinya bahaushiya tare da dirka mata ciki

Kungiyar kare hakkin musulmai a ranar Laraba ta zargi wani mutum mai suna Alex Chukwugo da laifin garkuwa da mutane, fyade da kuma dirkawa wata yarinya bahaushiya mai shekaru 18 ciki.

Kungiyar MURIC tayi ikirarin cewa, Chukwugo ya sace Mariam Dauda a watan Janairu na shekarar 2019 akan cewa ya aureta ba tare da sanin iyayenta ba. Kwatsam aka ganta da jariri a watan Oktoba da tace nashi ne, kamar yadda jaridar Tori.ng ta ruwaito.

A takardar da shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola yasa hannu, yace iyayen yarinyar na cikin tsananin rudani da rashin kwanciyar hankali a lokacin da aka sace yarsu.

Kungiyar musuluncin tayi kira ga gwamnatin jihar Legas da ta tabbatar da cewa Chukwugo ya fuskanci fushin hukuma.

Takardar itace kamar haka: "Wata yarinya bahaushiya mai shekaru 18 mai suna Maryam Dauda ta bace a watan Janairu,2019. Kwatsam bayan watanni sai aka ganta a gidan Alex Chukwugo dan kabilar Igbo. Duk da cewa, iyayenta sun samu labarinta tun a watan Yuni, basu samu ganinta ba sai a watan Oktoba da suka ganta a gidan Alex da jinjiri,"

DUBA WANNAN: Daga Amalala: Yayarta tayi mata mugun dukan da yayi ajalinta

"Wannan abun ashsha ne da takaici kuma ba za a lamunta ba. Alex Chukwugo ya sace yarinyar ne. A matsayinsa na dana Najeriya, Alex ya san yanda ake neman aure bisa ga al'ada amma yaki bin hakan saboda rashin gaskiya," in ji takardar

Takardar ta kara da cewa, "Yayi amfani da hanyoyin yaudara har yarinyar ta shiga gidansa a watan Janairu 2019. Ya killace yarinyar ba tare da son ranta ba kuma babu sanin iyayenta. A cikin wannan lokacin, iyayenta sun fuskanci rashin kwanciyar hankali,"

"Alex ya dinga wa yarinyar fyade har zuwa lokacin da ya kunsa mata ciki. Bai sanar da iyayenta ba sai bayan wata shida da batanta inda yazo da tsofaffi biyu yake sanar dasu ya ga yarsu. Ba tare da sun bayyana musu ko su waye ba, sun yi kamar jami'an tsaro har suka karba lambara wayar iyayen," cewar takardar.

"Sun sanar da iyayen cewa ba zaasu samu damar ganin yarsu ba. Makonni uku kenan da suka gayyacesu zuwa gidan da aka boye yarsu inda suka ganta da jinjirin da ta haifa. Sun bar gidan a fusace inda wani bahaushe ya tayasu kai kara ofishin MURIC. Bamu da wata mafita da ta wuce mu kaiwa 'yan sanda rahoto," takardar ta kara da cewa.

"Babu bata lokaci kuwa aka cafke wanda ake zargin a ranar 3 ga watan Nuwamba. A halin yanzu, da wanda ake zargin da wacce aka cutan suna gurin 'yan sanda a Ikeja. Amma kuma iyayen yarinyar sun ce an hana su ganin yarsu. Muna kira ga kwamishinan 'yan sandan jihar Legas da ya ja kunnen yaransa. Babu adalci a hana iyayenta ganinta." in ji takardar.

"Muna kira ga ma'aikatar shari'a ta jihar Legas da ta tsaya tsayin daka wajen fitarwa da yarinyar nan hakkinta.MURIC bazata gudu ba balle ja da baya. Sai an bi hakkin yarinyar nan da iyayenta." kamar yadda takardar tace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel