Makiyaya sun harbi dan sanda da manomi, sun kone kauye guda a jihar Jigawa

Makiyaya sun harbi dan sanda da manomi, sun kone kauye guda a jihar Jigawa

Wasu da ake zargin cewa Fulani makiyaya ne sun yi amfani da 'kwari da baka' wajen harbin wani dan sanda da wani manomi kafin daga bisani su kone wani kauye da ke karkashin karamar hukumar Kirikasama a jihar Jigawa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Kimanin tsawon wata guda kenan ana zaman 'dar-dar' a kananan hukumomin Kirikasama da Guru, saboda kwararowar wasu bakin Fulani makiyaya zuwa yankin, lamarin da yasa aka jibge jami'an 'yan sanda a yankin domin ganin ba a samu barkewar rikici ba.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa Daily Trust cewa makiyayan sun harzuka ne yayin da jami'an 'yan sandan da aka jibge suka yi kokarin korarsu saboda barnar da suke yi wa manoma a yankin.

Shaidar ya bayyana cewa bacin ran an nemi a kori Fulanin ne yasa suka kai wa dan sandan da manomin harin kwanton bauna da misalin karfe 8 na daren ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen kwamishinonin jihar Kano da ma'aikatunsu

Daily Trust ta wallafa cewa makiyayan sun yi amfani da kwari da baka a wajen harbin dan sandan a ciki da kansa, lamarin da ya jawo aka kwantar da shi a asibitin garin Nguru a jihar Yobe, yayin da shi kuma manomin ake duba lafiyarsa a gida.

A cewar shaidar, jami'an tsaro sun yi nasarar korar Fulanin amma bayan kamar sa'a daya da tafiyarsu sai suka dawo tare da kai hari kauyen Iyo, inda suka saka wa kauyen wuta.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, SP Abdul Jinjiri, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa dan sandan da aka harba ya samu lafiya, har ma ya dawo bakin aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel