An samu wata tsohuwar Nokia 3310 da caji 70% bayan shekara 20 tana kunne a ajiye

An samu wata tsohuwar Nokia 3310 da caji 70% bayan shekara 20 tana kunne a ajiye

- A lokacin da yake binciken wani mukulli a dakin shi, wani mutum ya gano wata tsohuwar wayar shi a cikin tarkace

- Mutumin ya gano tsohuwar wayar tashi mai kirar Nokia 3310 bayan shekara ashirin tana ajiye bai kula ta kanta ba

- Wani abin mamaki shine yadda ya samu wayar a kunne da caji 70% duk da irin wannan jimawar da tayi tana ajiye

Wani mutumi mai suna Kevin Moody daga garin Ellesmere Port, ya gano wata tsohuwar wayarshi Nokia 3310 a lokacin da yake binciken neman wani dan mukulli a dakin shi, a lokacin da yaga wayar tana kunne bayan shafe shekaru 20 yana nemanta.

Abin mamaki shine yadda wayar a wannan lokaci take dauke da caji har 70% duk da wannan jimawa da tayi a ajiye. Kevin cewa yayi shi ko cajar wayar ma bashi da ita ballantana yayi tunanin yi mata caji.

A wannan lokaci da wayoyi irinsu iPhone da suke shanye caji kamar suna shan ruwa, tsohuwar wayar nokia 3310 ita bama ta bukatar caji kwata-kwata.

KU KARANTA: Kuda wajen kwadayi: Ficik wata budurwa ta cirewa wani mutumi mazakuta da hakori a yayin da yake kokarin yi mata fyade

Masana sun bayyana cewa maimakon Nokia a wancan lokacin suyi wayar salula, kawai sun kirkiri wata sabuwar fasaha ce mai karfi.

Wasu sun bayyana cewa an kawar da wayar Nokia 3310 ne a wancan lokacin saboda an gano cewa za ta kashe kasuwar mai ganin cewa batirinta baya karewa hakan kuma na iya dukusar da kasuwar man.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel