Allahu Akbar: Kauyen da ya fi kowanne gari a duniya koyar da Al-Kur'ani mai girma

Allahu Akbar: Kauyen da ya fi kowanne gari a duniya koyar da Al-Kur'ani mai girma

Wani kauye dake yankin Amhara cikin kasar Habasha wacce aka fi sani da Ethiopia a yanzu, kauyen mai suna Shonke sun shahara matuka wajen koyar da Al-Kur'ani mai girma

Kauyen Shonke tsohon kauye ne mai dumbin tarihi, kamar dai yadda daya daga cikin limaman kauyen mai suna Hadji Mohammed yake bayyanawa wakilin BBC, ya ce:

"Kamar yadda muka samu labari daga wajen magabatanmu, cewa kauyen nan yayi shekara 900 da suka wuce a kwanan watan musulunci."

Argobbasawa ya bayyana cewa asalinsu Larabawa ne.

"Kalmar Argobba na nufin 'Larabawa sun zo', lokacin da Annabi Muhammadu (S.A.W) ya fara da'awar musulunci an samu tarzoma, sai suka zabi wasu suka turo su Habasha."

Kauyen dai yana da kofofi guda biyu saboda dalilin tsaro.

"Kamar yadda birane suke da tsaro a yanzu, muma haka muna da masu gadi a kofofin guda biyu."

Masallacin Shonke ya shahara wajen koyar da addinin musulunci.

KU KARANTA: Bidiyo: An kama almajirai da suke yaudarar mutane ta hanyar sanya ciwon karya a jikinsu don a basu sadaka

"Babu inda ya fi nan kyau da iya koyar da Al-Kur'ani, yadda ake koyarwa a nan tsohuwar hanya ce da ake koya addini."

Mazauna kauyen sun ragu da rabin yawansu a shekarun baya.

"Da can akwai kusan gidaje 500 a kauyen nan, amma yanzu gidaje 250 ne kacal."

Mutanen kauyen da yawa sun koma saman tsaunika domin su yi noma.

"Wannan shine kauyen magabatanmu, shine yasa muke son shi kuma zai yi wahala mu koma wani wuri da zama. Mun fi son gidajenmu da aka gina da duwatsu, ba ma son biranen nan masu kyalkyali. Burina shi ne wannan wurin mai tarihi ya cigaba domin 'yan bayanmu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel