Neman kudaden shiga: Gwmanatin Kaduna za ta fara safarar masara da citta zuwa kasashen Turai

Neman kudaden shiga: Gwmanatin Kaduna za ta fara safarar masara da citta zuwa kasashen Turai

Gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana kokarinta na sanya masara da citta cikin kayayyakin da zata dinga safararsu tare da cinikinsu a kasashen waje zuwa shekara 2020, kamar yadda babban sakataren ma’aikatar noma, Alhaji Sabiu Sani ya bayyana.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Sani ya bayyana haka ne yayin da yake kare kasafin kudin ma’aikatar na shekarar 2020 a gaban kwamitin noma na majalisar dokokin jahar, inda yace manufar ma’aikatar ya dace da manufar gwamnatin tarayya na inganta noma, samar da aikin yi da kuma rage radadin talauci.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Kano a fadar gwamnati

“Duba da rufe iyakokin Najeriya da gwamnati ta yi, a yanzu muna duba yiwuwar fara fitar da amfanin nomanmu domin samu karin kudaden shiga. Jahar Kaduna na daga cikin jahohin dake da arzikin citta da masara, idan har muka fitar da wadannan amfanin gona, hakan zai kara taimaka ma manomanmu.” Inji shi.

Daga karshe, kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati na yin iya kokarinta don ganin ta tallafa ma manoma a jahar ta yadda zasu kara ingancin amfanin gonarsu tare da kara adadin amfanin gonar da suke samarwa daga gonakansu.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin noma na majalisar dokokin Najeriya, Hassan Abubakar ya bayyana cewa kwamitin ta yaba da kokarin da ma’aikatar noman jahar take yi da kuma nasarorin da ta samu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel