A wani watan ina samun fiye da N100, 000 a sana'ar takalma – Khadijah Malumfashi

A wani watan ina samun fiye da N100, 000 a sana'ar takalma – Khadijah Malumfashi

Khadija Ahmed Malumfashi, Budurwace ‘Yar shekara 24 a Duniya wanda ta shiga cikin harkar hada takalman Maza da Mata. Khadijah ta yi hira da Daily Trust a game da wannan kasuwanci.

Wannan Baiwar Allah ta bayyanawa ‘yan jarida cewa ta shiga harkar takalma ne ganin yadda jama’a su ka fi maida hankalinsu a kan dinkin kaya. Kuma yanzu ta kan tashi da N10, 000 a wata.

Khadijah ta bayyana cewa ta shiga makarantar koyon dinkin takalma inda ta sake kwarewa. Ko can dama ta iya wannan aiki kafin ta zabi zuwa makaranta a sake yi mata wani horon na dabam.

Malama Khadijah ta bayyana cewa a cikin sa’a guda sai mutum ya hada takalmi. Wannan Matashiya tace abin da kuru make bukata shi ne kayan aiki kamar irin su fata, da leda da kirgi.

Yanzu haka Khadijah ta kan saidawa manyan dillalai ‘yan sari takalmanta a Garuruwan Kano, Katsina, Legas, Kaduna, Minna, Sokoto, Bauchi, Zamfara da wasu kewayen jihohin Najeriya.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun cafke masu garkuwa da mutane a Kebbi

Daga cikin kalubalen da Khadijah ta rika samu a wannan sana’a shi ne kayan aiki. A cewar ta kayan aiki su kan yi wahala duba da yadda jama’a su ke neman takalmanta daga fadin wurare.

A dalilin wannan ne Khadijah Malumfashi ta tattara ta bude wani wurin aikin a Legas domin an fi samun kayan aiki a can. Yanzu tace babu inda ba ta aika sakon takalmanta a fadin kasar nan.

Abin mamaki shi ne Khadijah ta fara wannan kasuwanci ne da N50, 000 rak. Amma yanzu a wani watan ta kan tashi da ribar N100, 000. A wasu watannin kuma kasa da haka ko kuma ma fiye.

Wannan Budurwa ‘yar asalin Malumfashi ta dauki hayar mutane hudu wadanda ke taimaka mata wajen hada takalman. Biyu su na aiki ne a shagon Legas yayin da sauran biyun su ke Kaduna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel