Majalisar dokokin Katsina ta tabbatar da yar’uwar Buhari da wasu a matsayin kwamishinoni

Majalisar dokokin Katsina ta tabbatar da yar’uwar Buhari da wasu a matsayin kwamishinoni

Rahotanni sun kawo cewa yar’uwar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Rabiatu Muhammed na daga cikin zababbu 17 da majalisar dokokin jihar Katsina ta tabbatar a matsayin kwamishinoni a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba.

Hajiya Rabia daga karamar hukumar Daura dake jihar ta kasance ‘ya ga marigayi babban yayan shugaba Buhari.

Ta kasance dauke da mukamin digiri na biyu a fannin kiwon lafiya da kuma wasu mukamai.

Sauran da aka tabbatar a matsayin kwamishinoni sun hada da Musa Adamu Funtua (Funtua LG); Yau Usman Gwajo- Gwajo (Mai’adua); Tasiu Dahiru Dandagoro (Batagarawa); Abdullahi Imam (Musawa); Dr.Rabe Wasiu ( Mani); Faruk Lawal Zobbe (Kankara); Mukhtar Gidado (Dutsinma); Abdulkadir Sani Aliyu Danladi (Katsina) da Farfesa Badamosi Lawal ( Charanchi).

Har ila yau an tabbatar da Abdulkadiri Zakka (Safana); Usman Nadada (Katsina); Kassim Mutallah (Funtua) Abdulkarim Yahaya ((Dutsi); Mustapha Mahmud (Ingawa); Yakubu Nuhu Danja ( Danja) da kuma Hamza Zuleima (Faskari).

Dandagoro, Faskari da Lawal sun kasance kwamishinoni masu dawowa yayinda suka yi aiki tae da Gwamna Aminu Masari a mulkinsa na farko.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Tasiu Musa-Maigari roki sabbin kwamishinonin da aka tabbatar da kada su ba Gwamna Masari kunya, inda ya kara da cewa gwamnan ya yarda da iyawarsu wajen yiwa jihar hidima.

KU KARANTA KUMA: Kwande na so Buhari ya roko malamai Larabawa daga kasar Saudiyya

Ana sanya ran za a rantsar da kwamishinonin a mako mai zuwa idan Gwamna Masari ya dawo daga ziyarar aiki da ya kai wajen kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel