Lafiya uwar jiki: Cire kasala da sirrika 8 na ganyen gwanda ga lafiyar dan Adam
Da yawan mutane su na da masaniyar amfanin gwanda ga lafiyar su, sai dai 'yan kalilan ne suke da ilimi akan alfanin ganyen itaciyar Gwanda.
Ganyen gwanda ya na dauke da sunadarai dake kawar da cututtuka irin su ciwon daji da makamantan su.
Wani bincike ya bayyana cewa, ganyen gwanda yana dauke da sunadarai irin su phytonutrients, dake habaka tafarkin rayuwar gami da bunkasa ta gudanar jini a jikin dan Adam.
Ganyen gwanda yana kunshe da sunadarai da suka hadar da; papain, alkaloid da kuma sunadarin chymopapain dake taka muhimmiyar rawar gani wajen dakile cutar kansa a jikin dan Adam.
KARANTA KUMA: Kiwon Lafiya: Illoli da kuma amfanin tsamiya a jikin dan Adam
A sakamakon arziki na wannan sunadarai, Legit.ng ta kawo muku jerin hanyoyin lafiya 9 da ruwan ganyen Gwanda ke ingantawa a jikin dan Adam.
1. Azurta jikin dan Adam da wadataccen jini. 2. Inganta lafiyar hantar dan Adam.
3. Inganta garkuwar jiki mai yaki da kwayoyin cututtuka irin su bacteria da Virus masu sanyan cutar Daji, zazzabin cizon sauro da makamantan su.
4. Cire kasala tare da karfafa gabobi da lakar jikin dan Adam.
5. Saukaka narkewar abinci da kuma tace shi daga cututtuka.
6. Hana kumburin jiki.
7. Inganta lafiyar zuciya tare da ba ta kariyar cututtuka.
8. Hana kamuwa da ciwon sukari ta hanyar daidaiton sundarin Insulin a jikin dan Adam.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng