Amfanin dabino 5 ga lafiyar bil Adama
Binciken masana da kwararrun kiwon lafiya ya tabbatar da cewa, kusan dukkanin dangin abinci ko na sha mai zaki da aka sarrafa na da matukar illa ga lafiya muddin aka yawaita ta'ammali da su, sai dai hakan bata kasance ga dabino ba.
Babu shakka dan dabino na da tabarrakin sunadarai masu tarin yawa da ke gagarumin tsarir wajen bunkasa lafiya da yi wa jikin dan Adam garkuwa ta kamuwa daga wasu miyagun cututtuka.
Dabino ya kushi sunadari kamar su; anthocyanidins, carotenoids, acetylcholine, magnesium, calcium, potassium da makamantansu. Sanadiyar wannan sunadarai, ga wasu cututtuka da dabino ya ke kawar wa daga jikin dan Adam:
1. Maganin gudawa
Dabino na maganin cutar gudawa da dukanin wasu cututtuka masu nabasa da ciwo ko lalacewar ciki da ake kamuwa da su.
2. Cutar Daji (Cancer)
Haka kuma dabino na maganin cutar nan ta ’Cancer’ mai kashe kwayoyin garkuwa.
3. Dabino na kara lafiya
Dabino na kara lafiya inda yake karawa mutum kiba saboda wasu sinadarai da yake kunshe da su. Haka kuma yana tsaftace jinin mutum daga kamuwa da cutar ciwon sikari ko kuma cutar hawan jini.
4. Dabino na kara karfi da kuzari
A dalilin irin sunadaran da ke ciki na Calcium, Sulphur, Iron da sauran su, Dabino na kara karfin kashi da kuma kwanjin mutum ya karu. Hakan ya sanya ake son fara cin dabino ga mai buda baki na sha ruwa bayan azumi domin kuwa yana kara karfi. Haka kuma ya sanya ake ba yaro da zarar an haife sa.
KARANTA KUMA: Cututtuka 10 da abarba ke magani a jikin dan Adam
5. Kara lafiyar kwakwalwa da kaifin basira
Dabino ya kunshi sunadaran Vitamin B da kuma Choline, masu taka rawar gani wajen bunkasa lafiyar kwakwalwa da kaifin basira. Haka kuma wannan sunadarai suna taimako wajen yin riga-kafin kamuwa da cutar mantau a yayin tsufa.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng