Akwai lauje cikin nadi: An tsinci gawa a Otal din wani tsohon gwamna

Akwai lauje cikin nadi: An tsinci gawa a Otal din wani tsohon gwamna

A ranar biyar ga watan Oktoba ne Peace Wisdom Ewinchola, saurayi mai shekaru 25 a duniya kuma ma’aikacin Grand Ibro Hotel Abuja ya isa wajen aikinsa. Lokacin da ya tashi aiki, dare yayi sosai, a don haka ne ya yanke hukuncin kishingida a daya daga cikin dakunan Otal din da ma’aikatan ke amfani dasu zuwa safiya.

Washegarin ranar da safe, ‘yan uwan aikinsa sun ga gawarsa a daki mai lamba 122 tare da wayarsa, kamar yadda rahoton wajen ajiye gawawwaki da jaridar Premium Times ta gani ya nuna.

Mutuwar ta girgiza ma’aikatan Otal din da ke Wuse Zone 5 tunda kuwa akwai manyan ofisoshin gwamnantin tarayya har uku dake kusa da wajen. Otal din ya kasance mallakin tsohon gwamnan jihar Kogi ne, Ibrahim Idris.

KU KARANTA: Yanzu - Yanzu: Buhari ya sauka Najeriya daga kasar Rasha

Yadda hukumar otal din ta dau kashe ma’aikacin ne ya kara jawo gunaguni fiye da mamakin mutuwarsa domin kuwa an fara zargin akwai wani abinda ake yunkurin boyewa.

Tambaya ta farko itaca, ta yaya gawar Ewinchola ta isa wajen ajiyar gawawwaki? Jaridar Premium Times ta gano cewa, gawar ta dade a dakin otal din ba tare da an sanar da jami’an tsaro ba. Lokacin da gawar ta isa asibiti cikin dare, ta samu rakiyar shugaban jami’an tsaro na otal din ne da wani mutum da yayi ikirarin shi sifetan ‘yan sanda ne. Amma kuma babu wani rahoto daga hukumar ‘yan sandan.

Kwanaki kadan jami’an ‘yan sanda suka garzaya asibitin don neman Karin bayani akan mutuwar domin basu da masaniya. Wani ne ya kirasu tare da basu bayanan sirri game da hakan.

A halin yanzu dai an tsananta binciken gano yadda mutuwar ta kasance kuma wanne boyayyen sirri ne a ciki.

Ma’aikatan otal din na cikin fargaba saboda wasu daga ciki sun ce ba wannan ne karo na farko da wani ya mutu a cikin zargin sarkakiya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel