Rage yakunewar fuska da sauran sirrika 8 na bawon ayaba ga lafiyar dan Adam

Rage yakunewar fuska da sauran sirrika 8 na bawon ayaba ga lafiyar dan Adam

Bawon ayaba yana kunshe da arziki na sunadaran gina jiki (nutrients) da kuma masu sanya karfin jiki (carbohydrates). Akwai ire-iren sunadaran vitamin B6, vitamin B12, magnesium da kuma Potassium wadanda suke da alfanu daban-daban ga lafiyar jikin dan Adam.

Ga jerin hanyoyi 9 da bawon ayaba ke inganta lafiyar jikin dan Adam.

1. Hasken hakori

Goga bawon ayaba ga hakora sau daya a kullum har na tsawon sati guda ko da kuwa na minti guda ne, yana matukar kalkale hakora su fita tar kamar haksen walkiya.

2. Fitar da tusar jaki

Mulka bawon ayaba yana taimakawa wajen ficewar tusar jaki da kuma hana bayyanar wat sabuwa a jikin dan Adam.

3. A matsayin ci ma.

amfani da bawon ayaba a matsayin abinci, domin kuwa mutanen kasar Indiya sun gano cewar sanyawa dahuwar kaza bawon ayaba yana kara laushin tsokar ta kaza.

4. Waraka ga kurajen fuska

Goga bawon ayaba ga kurajen fuska cikin minti 5 har na tsawon mako guda za a sha mamaki.

5. Rage yakunewar fata

Hada bawon ayaba tare da kwanduwar kwai kuma a shafa ga fuska sannan a wanke da ruwa, ya na matukar warware fata ta yi luwai-luwai.

KARANTA KUMA: Tsawa ta hallaka shanu 8 a jihar Ondo

6. Sauki ga buguwa a jiki

Shafa bawon ayaba ga wata buguwa ko wani ciwo na jiki yana taimakawa wajen rage radadin ciwon cikin gaggawa.

7. Waraka ga cutar makero

Bawon ayaba ya na taimakawa wajen kawar da cutar makero wadda turawa suke kiranta da Psoriasis. Ya na kuma taimakawa wajen rage radadin kaikayi na makeron

8. Cizon kwaruka

Shafa bawon ayaba akan cizo kamar na sauro yana dauke kaikayin zafin cizon

9. Kyalkyali

Goga bawon ayaba ga fatar takalmi, jakar leda ko azurfa yana sanya su zamto cikin kyalkyali a koda yaushe.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel