Wani dan bautar kasa ya yiwa wani yaro duka har lahira a Kano

Wani dan bautar kasa ya yiwa wani yaro duka har lahira a Kano

Rahotanni sun kawo cewa wani dan bautar kasa, a karamar hukumar Bebeji dake jihar Kano, ya yiwa wani yaro duka har lahira a daren ranar Alhamis.

An tattaro cewa lamarin ya afku a yammacin ranar Alhamis, lokacin da yaron ya yi shigan gaggawa fannin dakunan yan bautar kasar, domin karban kayan marmari daga mazauna wajen da kan rabawa yara kayan marmari.

Sai dai kuma, a yunkurinsa na karban nasa kason, sai yaron ya yi tuntube da wani dan bautar kasa, wanda hakan ya tunzura shi sannan ya dunga bugun yaron har sai da ya mutu.

Kakakin hukumar kawo sauyi na Bebeji, Shehu Suleiman wanda ya koro jawabin lamarin ga majiyarmu ta Punch, ta wayar tarho, yace jami’an yan sanda sun yiwa wajen kawanya, domin guje na yiwuwar karya doka da oda kan lamarin.

Har ila yau, ya bayyana cewa tuni jami’an yan sanda suka tafi da dan bautar kasar zuwa ofishinsu, yayinda aka dauki gawar yaron zuwa wani asibiti a yankin karamar hukumar Bebeji.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta tsare Maina a gidan kurkuku

Da aka tuntube shi ta wayar tarho, shugaban NYSC a Kano, Ladan Baba, ya tabbbatar da cewar sun samu labarin lamarin, inda yace tuni jami’ansa suka tafi Bebeji a safiyar Juma’a domin cigaba da binciken lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel