Jami’ar Kaduna ta fara binciken Malaman dake kwanciya da dalibai don cin jarabawa

Jami’ar Kaduna ta fara binciken Malaman dake kwanciya da dalibai don cin jarabawa

Jami’ar jahar Kaduna ta dakatar da wani jami’inta mai suna Bala Umar wanda ake kira da suna A.B Umar biyo bayan tuhumarsa da wata daliba ta yin a cewa ya taba nemanta da nufin lalata lokacin da yake jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa mahukuntan jami’an KASU sun kafa wata kwamiti da zata yi duba ga tuhumar da ake yi ma AB, sa’annan sun kafa wata kwamiti na daban da zata bincike aukuwar ire iren miyagun ayyukan nan a cikin jami’ar ta KASU.

KU KARANTA: A karon farko: Wani babban dan adawan gwamnati ya jinjina ma namijin kokarin Buhari

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ita dai wannan daliba da ba’a bayyana sunanta ba ta bayyana cewa jami’ar ABU ta sallami AB Umar ne a kan laifin neman lalata da dalibai mata, don haka take ganin bai kamata ya yi aiki a kowanne makaranta ba.

Mataimakin shugaba na biyu a KASU, Farfesa Abdullahi Ashafa ya bayyana cewa ba zasu lamunci irin wannan dabi’a daga wani malami ko jami’in jami’ar ba, kuma zasu dauki matakin daya dace a kan duk wanda aka kama da hannu ciki.

Ashafa yace: “Idan muka kama Umar da laifi, zamu bashi takardar gargadi, zamu sallameshi, sa’annan rabin albashinsa kadai zai iya samu, sai kuma mu mika rahoton bincikemu ga jami’ar domin ta yanke masa hukuncin daya dace dashi.”

Ita ma shugabar kwamitin na farko Farfesa Hauwa Evelin-Yusuf ta bayyana cewa aikinsa shine su bincike yadda aka dauki Umar aiki tare da abinda ya sabbaba barinsa jami’ar ABU. A yanzu haka dai an dakatar da Umar har sai an kammala gudanar da bincike a kansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel