Zakzaky ne kadai zai iya sulhu da gwamnatin tarayya - IMN

Zakzaky ne kadai zai iya sulhu da gwamnatin tarayya - IMN

Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wacce aka fi sani da Shi'a ta karyata rahoton cewa ta bude kofar sulhu tare da gwamnatin tarayya akan cigaba da haramta ayyukan kungiya.

Kungiyar tace shugabanta, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ne kadai ke iya shiga jarjejiyar sulhu tare da gwamnatin Tarayya da shugaban kasa.

A wani jawabin dauke da sa hannun Suhailah Ibraheem Zakakzaky a madadin shugaban IMN, kungiyar ta yi karin haske akan jawaban baya da aka danganta ga shugaban shi’a Mallam Yakubu Yahya Katsina, bisa shiga yarjejeniya da gwamnatin tarayya, inda ta bayyana cewa ba shi bane shugaban kungiyar.

Kungiyar ta jaddada cewa a bara kuma kafin tafiyar shugabanta zuwa Indiya gwamnatin tarayya ta nemi sulhu, sannan sai Zakzaky ya kafa wata tawaga domin ayi sulhu dasu. Tawagar farko sun hada da Farfesa Dahiru Yahya, Farfesa Abdullah Danladi, Dr. Yusha’u Shehu, Injiniya Yahya Gilima da kuma Injiniya Yunus Lawal.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta batar da kotu domin ta ba da umurnin kwace kadarorina

"A karo na biyu, wanda yazo kwanan nan kafin tafiyarsa zuwa ganin likita, Shugaban ya nada wadan mutanen: Farfesa Dahiru Yahya, Farfesa Abdullah Danladi, Malam Shuaib Isa Ahmad, Shaikh Halliru Maraya, Fasto Yohana Buru da kuma Farfesa Shehu Maigandi.

"Haduwa a karo na biyun ne yayi sanadiyyar da gwamnatin ta baiwa Sheikh da matarsa damar tafiya zuwa Indiya don ganin likta, ko da yake hukumomi sun dawo dasu haramtacciyar kurkuku ba tare da samun ganin likita ba.

"Idan Gwamnati na fatan cigaba da tattaunawa, toh ta emi tawaga ta biyu da shugaban kungiyar da kansa ya kafa," inji kungiyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel