CBN ta nemi bankuna su yi watsi da masu shirin kara kudin hawa shafin USSD

CBN ta nemi bankuna su yi watsi da masu shirin kara kudin hawa shafin USSD

Babban bankin Najeriya na CBN ya dauki matakin gaggawa a game da wani sabon tsari da kamfanonin sadarwa su ke neman shigo da shi.

Kamar yadda mu ka samu labari, wasu daga cikin manyan kamfanonin sadarwan da ke aiki a Najeriya sun fara yunkurin kara farashin USSD.

Gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele ya ba bankuna umarni cewa su yi watsi da duk wani kamfanin da ya kara kudin amfani da USSD.

Mutane kan yi amfani da tsarin USSD wajen aiki da bankunan su cikin sauki. A cikin karshen makon nan aka fara jin cewa za a kara kudin tsarin.

KU KARANTA: Buhari zai sa albarka wajen gagarumin taron Mawakan Afrika

Mista Godwin Emefiele ya fadawa bankunan kasuwa cewa su daina aiki da duk wani kamfanin sadarwa da ya ka hakikance a kan dada farashin.

Mai girma gwamnan babban bankin ya nemi bankunan Najeriyar su koma aiki da sauran kamfanonin sadarwar da su ba kara farashinsu ba.

Dazu nan mu ka ji cewa Ministan sadarwan Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami ya umarci kamfanonin da ke wannan shiri da su yi maza su janye.

Jaridar kasar nan ta Vanguard ce ta rahoto wannan labari. Mu na kuma sa rai cewa nan gaba za mu samu cikakken labarin daga bakin Kakakin CBN.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel