Kuma dai: Yanzun nan yan sanda sun sake kai mamaya wani gidan Mari a Kaduna

Kuma dai: Yanzun nan yan sanda sun sake kai mamaya wani gidan Mari a Kaduna

An shiga rudani a yankin gain Rigasa da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna biyo bayan wani mamayar sassafe da rundunar yan sandan Kaduna suka kai cibiyar horar da kangararru na Malam Niga a yankin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yan sandan sun tisa keyar mamallakin cibiyar, Lawal Yusuf Muduru zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Har yanzu babu cikakken bayani kan aikin yayinda motocin ya sanda ke jere a yankin Kwanar Gurguwa a Rigasa.

Majiyarmu ta tattaro cewa yan sanda sun kai mamaya cibiyar ne da sassafiyar yau Asabar, 19 ga watan Oktoba.

“Kwarai, yan sanda sun kai mamaya gidan da safiyar yau sannan sun kwashe fursunonin zuwa wani sansani a birnin. Yan sandan sun kuma tai da Malam Niga. Iya abunda zan iya fadi kenan a yanzu,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sandan Abuja sun cafke mutum 49 bisa zargin fashi da makami da kuma satar mutane

Duk kokari da aka yi domin jin tab akin kakakin rundunar yan sanda, DSP Yakubu Sabo ya ci tura, domin bai amsa kiran wayarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel