'Yan kai gawa sun ranta ana kare bayan kammala binne gawa sunji tana magana daga cikin kabari

'Yan kai gawa sun ranta ana kare bayan kammala binne gawa sunji tana magana daga cikin kabari

- Wani mutumi yayi mutuwar karya domin ya tsokani 'yan uwansa kuma ya sanya su dariya

- Ai kuwa haka aka yi domin kuwa a lokacin da kowa yake cikin jimami da kuka na rashin sa, kawai sai jin muryar shi aka yi tana fitowa daga cikin akwatin gawa

- Wannan bidiyo ya bai wa mutane da yawan gaske dariya, haka kuma da yawa sunyi ta tofa albarkacin bakin su game da bidiyon

A ranar 13 ga watan Oktobar nan ne wata mata mai suna Andrea Bradley ta sanya wani bidiyo a shafinta na sada zumunta na Facebok, inda aka nuno yadda ake yin zaman makokin mahaifinta.

Bradley wacce take zaune a kasar Ireland, ta bayyana cewa mahaifinta shakiyyi ne wanda a koda yaushe yake son yin abinda zai bada dariya, bidiyon dai ya bayyana yadda mahaifinta ya mutu.

Sai dai kuma a lokacin da 'yan uwa da abokan arziki suke ta faman kuka da jimamin mutuwar shi, kawai sai jin murya aka yi ta fito daga cikin akwatin gawa.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Yaro dan shekara 11 ya yiwa budurwa cikin shege har ta haihu

An jiyo mutumin yana cewa: "Ku bude ni na fito, akwai duhu sosai!"

Ga dai abinda aka rubuta a kasan bidiyon: "Ba shi da aiki sai tsokana da zolaya, tsokanar ka tayi daidai Baba, ka sanya mu dariya a lokacin da muke bukatar ta, ina sonka har abada."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel