Za mu tashi jami’ar jahar Kaduna daga inda take – Gwamnatin Kaduna

Za mu tashi jami’ar jahar Kaduna daga inda take – Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da manufarta na sauya ma jami’ar jahar Kaduna wuri daga inda aka santa zuwa kan babbar hanyar Zaria zuwa Rigachikun domin fadada jami’ar tare da baiwa dalibai damar samun isassun guraben karatu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kwamishinan ilimin jahar Kaduna, Shehu Mohammed Makarfi ne ya bayyana haka yayin wani taron babban zaure a kan kasafin kudin shekarar 2020 daya gudana a jahar.

KU KARANTA: Boko Haram: Dakarun Sojin Najeriya sun cigaba da samun narasa a kan yan ta’adda

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan yana cewa sauya ma jami’ar wuri zai baiwa mutane da dama damar kaiwa ga jami’ar cikin sauki, sa’annan yace nan bada jimawa gwamnatin za ta fara aikin gini a sabon wurin.

“Nan bada jimawa ba zamu tashi KASU zuwa filinta na dindindin a kan hanyar Zaria zuwa Rigachikun, an tanadar da filaye don wannan aiki, kuma nan gaba kadan zamu fara aikin gini a filin, sabon wurin zai fi dacewa da karatu da koyarwar dalibai.

“Wannan matakin zai baiwa dalibai karin guraben karatu a jami’ar, kamar yadda matakin kara yawan kwasa kwasai a kwalejin kimiyya da fasaha ta jahar dake Zaria zai haifar, haka zalika mun kara yawan kwasa kasai a kwalejin ilimi ta gidan Waya da kuma kwalejin horas da malaman jinya.” Inji shi.

A wani labari kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum guda biyo bayan wani mummunan hari da wasu miyagu yan bindiga suka kai a garin Birnin Gwari, cikin karamar hukumar Birnin Gwarin jahar Kaduna.

Kaakakin rundunar, DSP Yakubu Sabo ne ya tabbatar da haka a ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba, inda yace yan bindigan sun kai farmakin ne da misalin karfe 11: 30 na safiyar Laraba a wani gidan mai dake kauyen Doka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel