Kotu ta bukaci tsare malamin gidan horo na Daura tare da wasu mutane biyu a gidan yari

Kotu ta bukaci tsare malamin gidan horo na Daura tare da wasu mutane biyu a gidan yari

- Wata kotun majistare da ke zama a Katsina ta bukaci a aje mata Malam Bello, mai gidan horo da ke Daura tare da wasu mutane biyu a gidan maza

- A ranar 13 ga watan Oktoba ne aka kaiwa 'yan sandan yankin rahoton cewa 'yan gidan horon na yawo da mari a cikin gari

- Azabtarwa da cutarwar da ake musu ne tasa suka yi wa malamin bore tare da watsewa daga gidan horon

Wata kotun Majistare a Katsina ta bukaci adana malamin gidan horo na Daura mai shekaru 78 a gidan maza.

Za a aje Malam Bello ne a gidan yari har zuwa ranar 22 ga watan Oktoba, 2019 lokacin sa za a cigaba da shari’arsa.

Wadanda za a adansun taree sun hada da Habibu Bello mai shekaru 28 da Abba Abubakar mai shekaru 16.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana lokacin da dokar ilimi kyauta kuma dole zata fara aiki a jihar

A gurfanar da mutanen uku ne gaban kotun ne a ranar Talata akan zarginsu da ake da laifuka uku da suka hada da zaluntar yara da hadin kai wajen cutarwa.

‘Yan sandan sun sanar da kotun cewa ana zargin wadanda suka gurfanar din da yin karantsaye ga sashi na 97,257(b) da 238 na dokokin penal code.

‘Yan sandan sun sanar cewa, a ranar 13 ga watan Oktoba, 2019, sun samu labarin cewa ‘yan gidan horarwa na Daura sun yi bore ga hukumar gidan kuma an ga wasu daga cikinsu na yawo a gari da mari a kafa.

An sanar da kotun cewa, ‘yan gidan horarwar na zanga-zanga ne sakamakon zargin da suke na cewa ana musu cin zarafi kala-kala a gidan. Wannan cin zarafin ne yasa suka balle gidan marin tare da fita gari suna gudu da kacocin da aka dauresu.

Dan sandan da ke bincike akan lamarin, ASP Lawal Koran ya sanar da kotun cewa ana cigaba da binciken lamarin. Ya bukaci kotun da ta dage sauraron shari’ar.

Yayin duban bukatar dan sandan, alkalin y adage sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Oktoba inda za a yanke hukunci. Ya kuma bukaci da a tsare malamin da wasu mutane biyu a gidan maza har zuwa ranar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel