Bukatun Ma’aikatan Najeriya ya fi karfin Gwamnatin Tarayya - Inji Chris Ngige

Bukatun Ma’aikatan Najeriya ya fi karfin Gwamnatin Tarayya - Inji Chris Ngige

Gwamnatin tarayya ta fito karara ta bayyana cewa bukatun ‘yan kwadagon kasar game da karin albashi sun fi karfinta. Ministan kwadagon Najeriya, Chris Ngige ya bayyana wannan a jiya.

A Ranar Talata ne Dr. Chris Ngige ya bayyana cewa Najeriya za ta fuskanci irin matsalar da kasar Venezuela ta shiga idan har gwamnati ta biyewa bukatan da kungiyar ma’aikata su ke gabtarwa.

Ngige ya ke cewa ma’aikatan gwamnati miliyan 1.4 za su tashi da karin 33% a albashinsu a shekara mai zuwa muddin gwamnatin tarayya ta amince da abin da ke cikin bukatun kungiyoyin.

A jawabin na san a Ranar 15 ga Oktoba, Ministan ya hakikance a kan cewa an soma biyan ma’aikatan da ke kan rukuni na 1 zuwa 6 sabon tsarin albashi na akalla N30, 000 a fadin kasar.

KU KARANTA: Zaman NLC da TUC da Majalisa kan batun karin albashi ya gagara

Dr. Ngige yake cewa idan aka tattara kudin kasar aka biya albashi, gwamnati za ta kasance ba ta da kudin da za ta gina tituna da hanyoyin jirage da daukar nauyin kiwon lafiya da harkar ilmi.

Babban Ministan yake cewa babu abin da zai sa a jefa tattalin arziki gaba daya cikin matsala domin za a biya albashi. Wannan ya sa gwamnati da ‘yan kwadago su ka fara neman wata mafitar.

Za a cigaba da zaman da ake yi yau Laraba a birnin tarayya Abuja inda kungiyar kwadago ta NLC da ‘yan kasuwan Najeriya watau TUC su ke kokarin ganin an karawa manyan ma’aikata albashi.

Ministan ya nuna ba zai yadda ma’aikata su bankara gwamnati ba. Daga baya mun fahimci cewa kungiyoyin ma’aikatar sun fara saukowa daga kan matakin da su ke kai a baya game da karin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel