Wannan tsarin da Buhari ke bi shine ke haifar da rashawa - Clarke

Wannan tsarin da Buhari ke bi shine ke haifar da rashawa - Clarke

- Cif Robert Clarke ya yi raddi ga tsarin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Clarke yace shugaban kasar tamkar nakasasshe yake duba ga yanayin gwamnatin da yake jagoranta

- A cewar babban lauyan na Najeriya tsarin da Buhari ke bi shine ke haifar da rashawa

Wani Babban lauyan Najeriya, Cif Robert Clarke ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari tamkar nakasasshe ne duba ga yanayin gwamnatin da yake jagoranta.

Clarke, wanda ya kasance bako a shirin Channels Television na Politics Today, yace gwamnatin yau a Najeriya dake aiki da kudin tsarin mulkin 1999 wacce ta bari rashawa ke gina kanta a kowani ma’aikata ba zata iya yaki da cin hanci da rashawa ba.

A cewar Cif Clake, shugaba Buhari tamkar nakasasshe yake saboda wannan tsarin da yake gudanarwa shine ke haifar da rashawa.

“Kana da gwamnati dake yaki da rashawa alhalin tsarin da kake bi don yaki da rashawar na kara rura wutar rashawar,” inji Cif Clarke.

Ya bayana cewa ba za a iya kawar da rashawa ba saboda tana fitowa ne daga tsarin.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar lamari: Yar Mamman Daura ce ta dauki bidiyon Aisha Buhari tana fada

Da yake Magana game da yiwuwar mafita ga matsalar rashawa, Cif Clarke ya bayyana cewa tunda dai kundin tsarin mulki ne ke rayar da rashawa a Najeriya, toh ya zama dole a shafe ta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel