Bankada: Wani shafi dake yiwa Sadiya Farouq sojan gona yayi martani kan rade-radin auranta da Buhari

Bankada: Wani shafi dake yiwa Sadiya Farouq sojan gona yayi martani kan rade-radin auranta da Buhari

Wani shafin twitter da ke yiwa Sadiya Umar Farouq , ministar harkokin agaji da yaki da annoba sojan gona, yayi martani akan rade-radin da ke yawo game da auranta da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shafin twittan na bogi, @Sadiya_Farouq_, mai dauke da mabiya 462 ya sha banban da ainahin shafin ministar, @Sadiya_Farouq, wanda ke da mabiya 18,900.

Sai dai kuma shafin na bogi ya karyata jita-jitan, inda yayi sharhi akan labarin karyan.

“Akwai rade-radi da ake tayi a shafukan sadarwa dangane da aue tsakanina da Baba Buhari. Zan so na fayyace gaskiya cewa ni da Baba Buhari mun kasance abokai da dadewa sannan mai girma Aisha ta kasance aminiya kuma yar’uwata. Zan so wannan kyakyawar alaka ya cigaba,” cewar daya daga cikin rubutun da aka wallafa a shafin.

“Ya ku yan Najeriya, dan Allah kuyi watsi da dukkanin jita-jitan domin ba gaskiya bane. A yanzu haka mun mayar da hankalinmu kacokan kan yadda zamu tabbatar da Najeriya mai inganci. Mu cigaba da yiwa kasarmu Najeriya mai albarka addu’a. Allah yayi Albarka.”

KU KARANTA KUMA: Duka tatsuniyar gizo da koki ce: Bidiyon da ke yawo ba na kamun auren Sadiya Farouq da Buhari bane

Idan ba za ku manta ba a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba ne wani labari ya dunga yawo a kafafen sadarwa cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai auri ministar kula da harkokin agaji da annoba, Misis Sadiya Umar Farouq, a matsayin mata ta biyu.

Sai dai fadar shugaban kasa ta bakin hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ya karyata labarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel