Rufe iyakoki: Kwastan ta kama motoci 1,072 da buhunan shinkafa yar waje 19,000

Rufe iyakoki: Kwastan ta kama motoci 1,072 da buhunan shinkafa yar waje 19,000

Hukumar kwastam na Najeriya tace ta kama akalla motoci 1,072 daga hannun wasu da ake zargin masu fasa kauri ne tun bayan da aka rufe iyakokin Najeriya da na kasashen da ke makwabtakawa.

Kakakin hukumar, Joseph Attah ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 4 ga watan Oktoba a jihar Katsina lokacin wani taron wayar da kai akan shirin rufe iyakokin.

A cewar Attah an kama buhunan shinkafa yar waje guda 19,000, jarkokin fetur 4,765, tankunan Mai, bindigogi da dama,buhunan takin zamani NPK 131,mutane wadanda ba ‘yan Najeriya ba 146 da mutane 317 da ke da hannu a shigo da wadannan kaya kasar nan.

Ya ce gwamnati ta rufe iyakokin kasar nan ne domin hana aiyukkan ‘yan sumogal da shigowar mutanen da ba ‘yan Najeriya ba.

KU KARANTA KUMA: Satar dalibai: 'Dana zai cigaba da kasancewa a makarantar gwamnati – El-Rufai

Attah ya yi kira ga jama’a da su guji siyan kayan da ‘yan fasa kauri suka shigo da su , inda yace yin haka na gurguntar da tattalin arzikin kasar.

A baya hukumar Legit.ng ta rahoto cewa hukumar hana fasa kwauri ta kwastam ta yi kira ga dillalan motoci cewa su kwantar da hankalinsu a game da garkame gidajen motoci a jihar Kaduna da wadansu jihohin dake makwabtaka da ita.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastam, Mr Joseph Attah ne ya fitar da wannan jawabin ranar Laraba 3 ga watan Oktoba, 2019 a Kaduna jim kadan bayan hukumar ta kammala ganawa da kungiyar manoman shinkafa na Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel