Yadda bera ya sanya 'yan majalisa gudun famfalaki a fadar shugaban kasar Amurka

Yadda bera ya sanya 'yan majalisa gudun famfalaki a fadar shugaban kasar Amurka

- Wani bera da ya fado a kan cinyar wani dan jarida a fadar shugaban kasar Amurka ya zama abin magana a shafukan sada zumunta

- Beran ya fado daga saman rufin fadar shugaban kasar ne da misalin karfe 10:45 na safe

- Fadowar beran ta sanya mutane da yawa rantawa ana kare, yayin da wasu kuma suka yi ta maza suka kori beran ya gudu wani lungu

A ranar Talatar nan da ta gabata ne 'yan jarida suka ga wani abin mamaki, yayin da wani bera ya fado daga saman rufin fadar shugaban kasar Amurka wato 'White House'.

Beran dai ya fado akan cinyar wani wakilin jaridar NBC ne dake fadar shugaban kasar mai suna Peter Alexander, da misalin karfe 10:45 na safe.

Wasu daga cikin 'yan jaridar sun ranta ana kare, yayin da wasu kuma suka yiwa beran tara-tara domin su kama shi. Beran dai ya shiga ta wata kofa ne ya gudu abinsa, inda masu kaman shi din suka hakura bayan ya bace musu.

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda aka yiwa wasu 'yammata a makarantar sakandare bidiyo suna madigo a bainar jama'a

An dinga sanya hoton wannan bera a kafar sadarwa ta zamani, inda ya zama abin magana ga mutane.

Beraye, gafiyoyi, da kyankwaso dama sun jima da cika fadar shugaban kasar, domin kuwa a shekarar da ta gabata wani bera ya samu shiga fadar shugaban kasar, abinda ya saka aka sanya masu korar beraye a kowanne mako a fadar shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel