Jonathan: Wa’adin shekaru hudu ba zai isa Shugaban kasa ya yi tasiri ba

Jonathan: Wa’adin shekaru hudu ba zai isa Shugaban kasa ya yi tasiri ba

Tsohon shugaba, Goodluck Ebele Jonathan, ya ce gajeren wa’adin shugabannin kasashe ba za su isa a ga wani tasirin mai mulki a kasar ba. Sannan ya kuma soki masu dadewa a karagar mulki.

A wajen wani taro, Gooduck Jonathan wanda ya mulki Najeriya ya bayyana cewa babu bukatar shugaban kasa ya yi shekara 14 ko fiye a kan mulki domin kuwa kasar jama’a ba gidansa bane.

Dr. Jonathan ya yi wannan bayani ne a wajen taron da aka shirya a kan wa’adin mulki a babban birnin kasar Nijar na Niamey. Tsohon shugaban ya kuma koka da kudin da aka kashewa a siyasa.

A na sa ra’ayin, Jonathan ya na ganin cewa irin tarin kudin da ake narkawa wajen lashe zabe za su iya sa mai mulki ya karkatar da hankalinsa musamman a kasashenmu masu kokarin tasowa.

Jonathan yace yanzu tuni har an fara maganar zaben 2023 a Najeriya duk da kwanan nan aka kammala rikicin 2019 inda ya ke ganin cewa shirya zabe duk bayan shekaru 4 abu ne mai tsada.

KU KARANTA: Kamar in kashe kai na a lokacin da na bar ofis - Jonathan

A jawabin da Goodluck Jonathan ya yi, ya bada misali da shugaba Farfesa Wade wanda ya kara wa’adin shugaban kasa a Sanagal da tunanin zai zarce a mulki, a karshe kuma bai yi nasara ba.

“Amma Macky Sall ya rage wa’adin zuwa shekaru hudu. Dole mu yabawa shugabanni irin wadannan.” Inji Jonathan wanda ya kara da: “Babu dalilin mutum 1 ya yi ta mulki na shekara 14.”

Tsohon shugaban na Najeriya ya ke cewa: “Shekaru 14, ka na yin mene? Kasar ba daular gidan ka ba ce. Kasashe su na da damar canza dokokinsu, kamar yadda shugaban kasar Nijar ya fada.”

“Mafi yawan Kasasehn Afrika su na koyi ne da Amurka inda su ka dauko wa’adin shekaru hudu Kasashen nan sun hada da Najeriya, Kenya, da Ghana. Shekara hudu ya yi kadan a kasashenmu.”

“Zabe kan karkatar mana da hankali. A kan menene za a rika kashe kudi duk bayan shekaru hudu don a zabi shugaban kasa.” Inji Jonathan wanda ya so ya maida wa’adi shekara shida a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel