Yadda fitaccen dan kwallon kafa Sadio Mane ya ginawa Musulmai Makaranta, Masallaci da Asibiti a kasar Senegal

Yadda fitaccen dan kwallon kafa Sadio Mane ya ginawa Musulmai Makaranta, Masallaci da Asibiti a kasar Senegal

- A yayin da abokanan shi na kwallon kafa suka shiga duniya domin jin dadi da hutawa

- Shi kuma fitaccen dan wasan kwallon kafar na kungiyar Liverpool zuwa yayi kauyensu na Bambali yana kallon irin yadda ake yin aikin da ya bayar ayi

- Sadio Mane ya bayar da aikin gina Masallaci, Makaranta, da asibiti a mahaifarsa inda ya taso tun yana karami

Fitaccen dan wasan nan na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, dan kasar Senegal, Sadio Mane ya gina Makaranta, Masallaci da Asibiti a kasar sa ta Senegal. A lokacin da abokanan sa suka shiga duniya suke jin dadinsu, shi kuma an hango shi yana duba yanayin yadda aikin da ya bayar yake tafiya a garin Bambali na kasar Senegal din.

An haifi Mane a watan Afrilun shekarar 1992, yana buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta kasar Senegal, sannan kuma yana bugawa da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool. Yana yin wannan gagarumin aiki ne a mahaifarsa ta Bambali, inda ya taso yayi rayuwa.

Ya yiwa mutanen garin nasa Masallaci, Makaranta da Asibiti. Haka kuma ya dauki nauyin wasu ayyuka da dama a garin dama kasar ta Senegal baki daya. An bayyana cewa ya bayar da kimanin naira miliyan dari (N100m) domin a gina makarantar firamare ga yaran garin na Bambali.

KU KARANTA: Allahu Akbar: Wata Kirista kenan da ta Musulunta ta kuma Musuluntar da danginta gaba daya da kuma abokanan ta sama da 30

Sadio, wanda yake cikakken Musulmi yaki yayi magana akan wannan ayyukan alkhairi da yake yi, inda ya bayyana cewa shi yana yi ne saboda irin soyayyar da yake yiwa mutanen shi ba wai domin duniya ta gani ba.

Sadio Mane ya bayyana kansa a matsayin mutum mai kokarin koyi da addinin Musulunci. Shi da abokinsa na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohamed Salah, ya zama abin kwatance saboda riko da addini da yake dashi wanda baya boyewa a ko ina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel