Cika shekaru 59 da samun 'yanci: Abubuwa 10 a kan Najeriya da ya kamata kowa ya sani

Cika shekaru 59 da samun 'yanci: Abubuwa 10 a kan Najeriya da ya kamata kowa ya sani

A yayin da aka fara gudanar da al'amuran bikin tuna wa da cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yanci, Legit.ng ta kawo muku wasu jerin muhimman abubuwa 11 a kan Najeriya da ya kamata duk dan kasa ya sani.

1. Najeriya ce kasa ta 32 a cikin jerin kasashen duniya da ke da girman kasa, girman kasar Najeriya ya kai 923,768 km2 (356,669 sq mi)

2. Marigayi Benedict Odiase, mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai ritaya, shine wanda ya kirkiri kidan taken Najeriya da ake amfani da shi

3. Mutane hudu ne suka hada kalmomin taken Najeriya, mutanen sune; Dakta Omoigui, John Ilechwukwu, Eme Etim Akpan, B. A Ogunnaike da P. O Aderibigbe

4. Akwai jami'o'in gwamnatin tarayya 37, 37 mallakar jihohi da kuma fiye da 50 masu zaman kansu

5. Kididdigar jama'a ta karshe da aka yi a shekarar 2006 ta nuna cewa akwai mutane miliyan 140,431,790 - duk da yanzu kiyasi ya nuna cewa akwai a kalla mutane 170,000,000 a Najeriya

DUBA WANNNAN: Cika shekaru 59 da samun 'yanci: Trump ya rubuto wa Buhari wasika, ya fadi bukatarsa

6. Flora Shaw, matar Lord Lugard, ita ce wacce ta kirkiri sunan 'Nigeria'. Lugard na daya daga cikin turawan da suka mulki Najeriya a karkashin mulkin mallaka.

7. Najeriya ce kasa ma fi yawan jama'a a nahiyar Afrika, sannan kasa ta bakwai a yawan jama'a a duniya.

8. A ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 1901, kasar Ingila ta mayar da Najeriya karkashin mulkinta

9. An yi yakin basasa ma fi tsawo a Najeriya daga ranar 6 ga watan Yuli na shekarar 1967 zuwa watan Janairu na shekarar 1970, watanni 30 kenan.

10. Najeriya ta kasance a karkashin mulkin soji na tsawon shekaru 33, daga shekarar 1966 zuwa 1999.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel