Baya goya marayu: Masu ritaya 1000 sun samu kudin sallamarsu a Borno

Baya goya marayu: Masu ritaya 1000 sun samu kudin sallamarsu a Borno

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ya amince da biyan kudin sallama ga rukuni na biyu na wadanda suka yi ritaya mutum 1,000 tsakanin 2013 zuwa yanzu.

Wannan yana zuwa ne watanni biyu bayan gwamnan ya saki wasu kudade domin biyan kudin sallama ga rukunin farko na masu ritaya wanda ke dauke da mutane 1,684 a mukamai mafi karanci wadanda suka yi ritaya tsakanin 2013 zuwa Yuni 2019.

Yayinda yake gabatar da sanarwa a madadin gwamnan, hadimin gwamnan, Malam Isa Gusau ya bayyana a jawabinsa a ranar Lahadi, 29 ga watan Satumba cewa an tura kudade zuwa asusun bankunan masu ritaya 1,000.

Ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka yi na biyan kudin sallamam masu ritaya wanda ya taru, tabbas za a biya.

KU KAANTA KUMA: An zo wurin: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukuncin a shari'ar zaben gwamnan jihar Sokoto

Hadimin duk da haka ya fahimci cewa a halin yanzu, kudin fanso na wata-wata da jihar Borno ke biyan masu ritaya ya faa ne tun shekaru takwas din da suka gabata.

Kudin sallama da fanso sun kasance shirin dake karkashin kulawar gwamnati don samar da hanyar cin abinci ga ma’aikata bayan sunyi ritaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel