Murnar cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yancin kai: Gwamna Fintiri ya gafarta wa Fursunoni 18 a jihar Adamawa

Murnar cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yancin kai: Gwamna Fintiri ya gafarta wa Fursunoni 18 a jihar Adamawa

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, ya bayar da lamunin sakin wasu fursunoni 18 da ke cin sarka a gidajen kaso daban-daban a jihar a yayin murnar cikar kasar Najeriya shekaru 59 da samun 'yancin kai.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, gwamnan cikin wata sanarwa da ya gabatar a ranar Litinin, ya ce wannan yunkuri na kan tafarkin kundin tsarin mulkin kasa wanda ya ba shi damar yin afuwa ga masu laifi.

Hadimi na musamman ga gwamna Fintiri a kan kafofin sadarwa, Mr Solomon Kumangar, shi ne ya gabatar da wannan sanarwa yayin zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Yola.

Mr Kumangar ya ke cewa, "domin murnar cikar Najeriya shekaru 59 da samun 'yancin kai, gwamna Fintiri ya ba da umarnin sakin wasu fursunoni 18 da ke bai wa duga-dugansu hutu a gidajen kaso 5 daban-daban a fadin jihar Adamawa".

KARANTA KUMA: Tabbas akwai damuwa a ofishin mataimakin shugaban kasa Osinbajo - SMBLF

"Wannan yayi daidai da tanadin sashe na 22 cikin kundin tsarin mulkin kasa wanda ya bai wa gwamnan damar yin afuwa ta ganin dama ga wadanda suka aikata laifi."

Ya ce fursunonin da za a 'yantar sun kasance zababbu daga gidajen kaso na Yola, Numan, Ganye, Jada da kuma Kojoli.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel