Yansanda sun gano wani gida da aka daure yara 300 a cikin sa a Kaduna

Yansanda sun gano wani gida da aka daure yara 300 a cikin sa a Kaduna

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kaduna sun bankado wani gida a cikin garin Kaduna da aka tara yara masu kananan shekaru da masu matsakaita shekaru, wasunsu kuma daure da mari.

Gidan talabijin na TVC ta ruwaito an gano wannan gida ne a unguwar Rigasa dake cikin karamar hukumar Igabi, daga cikinsu akwai kananan yara da basu wuce shekaru 10 ba, inda yaran suka tabbatar da cewa ana yin luwadi dasu.

KU KARANTA: Daga karshe El-Rufai ya fara biyan karancin albashi a jahar Kaduna

Yansanda sun gano wani gida da aka daure yara 300 a cikin sa a Kaduna
Yaran
Asali: Twitter

Haka zalika kananan yara sun fallasa cewa ana tilasta musu yin azumi ba a son ransu, amma dai an yi sa’a kwamishinan Yansandan jahar, Ali Janga ya isa wajen, kuma sun dauke da yaran daga gidan, sa’annan zasu kaddamar da bincie.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an samu wasu yara masu matsakaicin shekaru da aka samesu da mari a kafafuwansu, sai dai mutanen da suka tara yaran a gidan sun bayyana cewa gidan horo ne, ma’ana suna horas da kangararrun yara ne.

Yansanda sun gano wani gida da aka daure yara 300 a cikin sa a Kaduna
Yaran
Asali: Twitter

Wata majiya daga rundunar Yansandan tace wasu daga cikin daliban sun taho ne daga kasashen Burkina Faso, Mali da wasu jahohin kasashen Afirka.

A wani labari kuma, gwamnanatin jahar Kaduna ta fara biyan karancin albashin N30,000 kamar yadda gwamnan jahar, Nasir Ahmad El-Rufai ya yi alkawari tun a farkon watan Satumba.

Gwamnan jahar Kaduna ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace: Mun yi alkawari za mu fara biyan mafi karancin albashi a wannan wata na Satumba, kuma cikin ikon Allah mun cika wannan alkawarin.”

Yansanda sun gano wani gida da aka daure yara 300 a cikin sa a Kaduna
Yansanda
Asali: Twitter

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel