Buhari ya kaddamar da lambar ko ta kwana da 'yan Najeriya zasu kira a halin bukatar agajin gagga wa

Buhari ya kaddamar da lambar ko ta kwana da 'yan Najeriya zasu kira a halin bukatar agajin gagga wa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da lambar 'ko ta kwana', 112, da 'yan kasa zasu kira a halin bukatar agajin gagga wa (ECCs) a ko ina suke a fadin Najeriya.

An kaddamar da lambar ne a jihar Katsina, kuma ministan sadarwa, Dakta Ali Ibrahim Pantami, ne ya wakilici shugaba Buhari a wurin kaddamar da lambar, wanda aka yi ranar Litinin.

Pantami ya bayyana cewa an dade da saka batun kaddamar da lambar a cikin tsarin aikin gwamnatin tarayya, amma sai yanzu gwamnatin Buhari ta kaddamar da aikin.

DUBA WANNAN: Buhari ya kaddamar da lambar ko ta kwana da 'yan Najeriya zasu kira a halin bukatar agajin gagga wa

Buhari ya bawa 'yan Najeriya tabbacin cewa hukumar kula da kafafen sadarwa (NCC) za ta cigaba da taka muhimmiyar rawa wajen bayar da gudunmawa ga 'yan kasa da ke bukatar agajin gagga wa tare da yin kira ga jama'a da su yi amfani da sabon cigaban ta hanyar da ya dace.

Ya ce sabon cigaban zai taimaka a bangaren yaki da cin hanci da rashin tsaro tare da inganta tattalin arzikin kasa ta hanyar samar da aiyuka.

Da yake jawabi yayin kaddamar da lambar, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda mataimakinsa, Alhaji Mannir Yakubu, ya wakilta, ya ce lambar za ta bawa 'yan Najeriya damar isar da sako a lokacin da suke bukatar agajin gagga wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel