Sojoji sun yi alwashin gamawa da Boko Haram idan suka shiga garin Maiduguri

Sojoji sun yi alwashin gamawa da Boko Haram idan suka shiga garin Maiduguri

Rundunar Sojan kasa ta Najeriya ta dauki alwashin idan har mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka shiga garin Maiduguri toh kashinsu ya bushe, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito rundunar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa data fitar, inda take tabbatar ma jama’a cewa babu wani shiri da Boko Haram ke yi na kai hari cikin Maiduguri, don haka kowa ya kwantar da hankalinsa.

KU KARANTA: Kali yadda Sojojin Najeriya suka gasa wani mutumi da wuta kamar kaza

An samu zaman dar dar tare da fargba a kwanakin baya sakamakon yawaitan artabu tsakanin Sojoji da Boko Haram a yankunan dake kusa da garin Maiduguri, babban birnin jahar Borno, amma duk da haka rundunar Soji tace batun harin Boko Haram ba gaskiya bane.

Mataimakin kaakakin rundunar Sojan kasa, Ado Isa ne ya tabbatar da haka, inda yace a shirye Sojoji suke su ragargaji mayakan Boko Haram idan har suka shiga garin Maiduguri, a cewarsa:

“Labarin dake wanzuwa a kafafen sadarwar zamani ya nuna wai mayakan Boko Haram suna shirin kai hari a wasu yankunan garin Maiduguri dake dauke da mutane da dama, don haka shelkwatar tsaro dake yaki da Boko Haram na Lafiya Dole na tabbatar ma jama’a cewa an dauki matakan hana faruwar hakan.

“Haka zalika Sojojinmu a shirye suke don dakile duk wani motsin yan ta’adda, bugu da kari Sojojin Najeriya na cikin azama da shirin kota kwanan saukan ma yan ta’addan ruwan bala’i da zarar sun yi kokarin shigowa.” Inji shi.

Daga karshe Ado Isah ya yi kira ga jama’a dasu yi watsi da rahoton a matsayin jita jita, inda yace wadanda basu son zaman lafiya ne da abokna Boko Haram ne suke yada wannan jita jita domin su tsoratar da jama’a, sa’annan ya shawarci jama’a dasu kasance masu sa ido a unguwanninsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel