Ana bikin duniya ake na kiyama: An kayata kabarin da za a binne Robert Mugabe, an sanya na'urori da kayan ado

Ana bikin duniya ake na kiyama: An kayata kabarin da za a binne Robert Mugabe, an sanya na'urori da kayan ado

- Wani labari da yake ta yawo a kafafen sadarwa kwanakin baya akan tsohon shugaban kasar Zimbabwe Rober Mugabe sun karawa sama hazo

- Inda aka bayyana hoton wata akwatin gawa da aka kayata ta da na'urori da kayan kyale-kyale aka bayyana cewa a ciki za a sanya shi

- Mutanen da suka kera akwatin nashi sun bayyana cewa sam-sam zancen ba haka yake ba, sun dai bayyana cewa sun saka wasu sinadarai a cikin akwatin ta yadda zai shafe shekara 10 bai rube ba

Kwanaki kadan da suka gabata akwai labarai da aka dinga wallafawa dangane da akwatin da za a sanya Robert Mugabe a ciki, yadda aka kawata ta da na'urori masu kwakwalwa da kuma abubuwa na yanar gizo, inda aka bayyana cewa an kashe kudi kimanin naira biliyan 17, sai dai an gano cewa duka wannan labarin kanzon kurege ne.

Wannan labarin da ake yadawa dangane da shugaban kasar labarin karya ne, saboda akwatin da aka sanya an samo ta ne wani shafin yanar gizo-gizo tun a shekarar 2007, inda aka hada wata na'ura mai kwakwalwa da siffar akwatin gawa.

KU KARANTA: Allah ka bamu mata na gari: Bayan shafe shekara 10 yana wahala da yaron tun yana jariri har ya girma, mahaifin ya gano cewa ashe yaron ba nashi bane

Wannan labari da aka yada ya bayyana cewa an kashewa gawar wannan makudan kudade ne, saboda idan aka binne shi, iyalan shi zasu dinga kallon abinda zai dinga faruwa da gawar shi a wayoyinsu.

Sai dai kuma a cewar wasu masu hada akwatin gawa na birnin London, sun ce: "Wannan labari ba gaskiya bane, amma dai an hada wasu abubuwa a cikin akwatin marigayin, wanda zai saka gawar shi baza ta rube ba daga nan zuwa shekara goma, haka kuma ga iyalan shi da suke son ganin gawarshi a lokacin da yake cikin kabari zasu iya yin hakan ta hanyar amfani da wayoyinsu na hannu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel