Allah daya gari ban-ban: Kabilar da saurayi zai shiga har gidan uban budurwa ya sace ta kafin daga baya yaje ya nemi iyayenta su aura masa ita

Allah daya gari ban-ban: Kabilar da saurayi zai shiga har gidan uban budurwa ya sace ta kafin daga baya yaje ya nemi iyayenta su aura masa ita

- Kabilar Latuka kabila ce dake can yankin Kudancin Sudan dake cikin nahiyar Afrika

- kabilar suna da wata al'ada a fannin aure, ta inda saurayi zai je ya sato budurwa kafin a bashi damar ya aureta

- Haka kuma idan saurayin ya sace budurwar sai yaje ya koma wajen ubanta ya nemi aurenta, shi kuma uban zai dauki bulala ya daki saurayin, hakan shine alama dake nuna cewa uban ya amince da saurayin ya auri 'yarshi

Kabilar Latuka kabila ce da ta yadda duk saurayin da yaga budurwa yake so to sai ya fara shiga gidan ubanta ya sace ta, sannan daga baya sai yaje wajen iyayenta ya nemi su aura masa ita.

Wasu abubuwa guda biyu dangane da kabilar Latuka wadanda suke baiwa mutane mamaki sune:

Na farko dole ne sai saurayin da yaga budurwar yaji yana so ya shiga har gidan ubanta ya satota ta karfin tsiya yaje ya boyeta.

KU KARANTA: Kunji wata kuma: Banyi imani da 'Bible' ba saboda cike yake da labaran gizo da koki - Kemi Olunloyo

Na biyu kuma dole ne mahaifin yarinyar da aka sace ya doki saurayin da yake so ya auri yarinyar tashi, ita ce hanya guda daya dake nuna cewa mahaifin yarinyar ya yarda da saurayin ya auri 'yar tashi, idan bai yadda ba bazai dake shi ba.

A yayin da mu a Najeriya kasar Hausa idan za'ayi aure kowa yake zama cikin farin ciki da annushuwa tsakanin ango da amarya, su kuma kabilar Latuka da sure kudancin kasar Sudan dake cikin Afrika ba haka al'adar take a wajensu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel