Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Wani mutum ya fille kan dan achaba, ya kuma cire kayan cikinsa a jihar Neja

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Wani mutum ya fille kan dan achaba, ya kuma cire kayan cikinsa a jihar Neja

Rundunar yan sanda sun kama wani da ake zargin matsafi ne, Tunde Tayo na Ungwan Roka, Maitumbi, Minna a karamar hukumar Bosso da ke jihar Niger, bisa zargin kashe wani mutum sannan ya binne shi a kangon gidansa bayan ya cire masa kai.

An kama Tayo ne bayan ya fille kan mutumin wanda ya kasance dan achaba, sanan ya cire zuciya da kayan cikisa a yankin Crystal FM da ke Maitumbi.

Newtelegraph ta ruwaito cewa matashin da aka kashe mai shekara 25 a duniya, Abdullahi Salle, ya kasance dan achaba.

An tattaro cewa jami’an yan sanda da ke reshen Maitumbi ne suka kama Tayo mai shekara 30 bayan ya kashe dan achaban wanda ya kasance dan Ungwan Rama domin yayi asiri dashi.

Da yake amsa tambayoyi, mai laifin yayi ikirarin cewa yana gyara ciyayin da suka tashi ne a gini kafin aka kama shi.

KU KARANTA KUMA: Bazan iya wannan masifar ba nima fita zanyi daga Kannywood wallahi - Teema Makamashi

Bayan an ci gaba da bincike sai aka gano cewa mai laifin ya binne gawar Salleh a cikin wani babban rami da ke kusa da gidansa.

Mai laifin yace ya yaudari mutumin zuwa kangon gininsa da ke Ungwan Roka, inda ya aikwatar da mummunan ta’asar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel