Yarinyar da ta fi kowa kyau a duniya ta girma ta wallafa wasu sababbin hotuna

Yarinyar da ta fi kowa kyau a duniya ta girma ta wallafa wasu sababbin hotuna

Yarinyar da aka yi ittifakin cewa babu wacce ta kai ta kyau a duniya ta girma yanzu, inda ta dauki wasu sabbin hotuna ita da saurayinta a lokacin da suka fita yawan shakata a birnin Los Angeles na kasar Amurka

Yarinyar da ta fi kowa kyau a duniya ta girma ta wallafa wasu sababbin hotuna
Thylane
Asali: Facebook

Thylane Blondeau, yarinya ce da aka taba bayyana cewa babu macen da ta kai ta kyau a duniya, yanzu haka dai ta girma sosai ta zama budurwa, kuma an dauki hotonta a lokacin da ta fita yawon shakatawa da saurayinta mai suna Milane Meritte a birnin Los Angelas.

Yarinyar da ta fi kowa kyau a duniya ta girma ta wallafa wasu sababbin hotuna
Thylane and Milane
Asali: Facebook

Masoyan guda biyu sunyi kyau sosai a yayin da aka dauki hoton Milane ya kwanto da kanshi yana kokarin sumbatar Thylane a kumatu a lokacin da suka shiga wani shagon sayar da kaya a birnin Los Angeles na kasar Amurka a ranar Larabar nan.

Yarinyar da ta fi kowa kyau a duniya ta girma ta wallafa wasu sababbin hotuna
Thylane and Milane
Asali: Facebook

KU KARANTA: Awanni kadan da dawowar 'yan Najeriya, 'yan kasar Afrika ta Kudu sun koma kashe 'yan Pakistan

Thylane, wacce ta cika shekara 18 a duniya, tayi suna a duniya tun lokacin da take yarinya karama, kayan da ta saka ya nuna irin yanayin halittar da Allah yayi mata ta kira mai kyau da kyan diri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng