Boko Haram: Sojoji 9 sun mutu, an nemi 20 an rasa bayan wani gumurzu da yan ta’adda

Boko Haram: Sojoji 9 sun mutu, an nemi 20 an rasa bayan wani gumurzu da yan ta’adda

Akalla dakarun Sojin Najeriya guda 20 dake aikin tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso gabas a karkashin Operation Lafiya Dole ne suka yi batan dabo bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kai ma Sojoji a Borno.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito baya ga bacewar Sojoji 20, an tsinci gawarwakin wasu Sojoji guda 9 bayan harin da yan ta’addan suka kai musu a kauyen Granda dake cikin yankin Gudumbali na jahar Borno.

KU KARANTA: Budurwa yar Kaduna ta gamu da hukuncin bulala 80 saboda shan tabar wiwi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan Boko Haram sun shirya harin kwantaun bauna ne a kan sansanin Sojojin Najeriya a daidai kauyen Granda da tsakar daren Litinin, inda aka yi ta musayar wuta har zuwa safiyar Talata, 10 ga watan Satumba.

Majiyar ta cigaba da fadin duk da cewa Sojojin sun samu agaji daga dakarun rundunar Sojan sama da suka taimakesu da jirage yaki, amma duk da haka Sojoji da dama sun tsere daga harin, wanda hakan ya baiwa yan ta’addan daman kama sansanin.

Majiyarmu ta bayyana wani rahoto daga gidan talabijin na Channels wanda tace Sojoji 7 daga cikin guda 9 da Boko Haram ta kashe yankan rago ta yi musu, a yanzu haka dai an kwashe gawarwakin Sojojin zuwa asibitin Sojoji dake Maiduguri.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa bayan sun fatattaki Sojojin, yan ta’addan sun yi awon gaba da tankar mai guda daya, da kuma wasu kananan motoci daban daban.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto hukumar Soji ba ta ce uffan game da hari ba, amma rahotanni sun bayyana cewa Boko Haram ta yi amfani da wasu yan leken asiri ne wajen samun bayanai game da Sojojin tare da sabon sansanin nasu dake Gudumbali.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel