Tirkashi: Naga abubuwa da yawa a lahira da mutane baza su so jin labarin su ba - In ji Likitan da ya mutu ya dawo

Tirkashi: Naga abubuwa da yawa a lahira da mutane baza su so jin labarin su ba - In ji Likitan da ya mutu ya dawo

- Wani likita da ya wallafa labarin shi na cewa ya mutu ya dawo ya bayyana yadda aka zare ranshi daga jikin shi

- Ya ce lokacin da ya fara rashin lafiya ya san cewa mutuwa zai yi hakan yasa ya kira 'yan uwansa domin ya basu wasiyya, kawai sai ji yayi an zare ranshi

- Ya ce ya tashi ya ganshi a wata duniya daban, inda kuma daga baya ake fada mishi cewa yanzu lokacin shi bai yi ba, dan haka aka dawo masa da ruhinsa

Wani likita ya bada labarin abubuwan da ya gano bayan ya dawo daga wata 'yar karamar mutuwa da yayi, sai dai kuma labarin nashi ya bar masu amfani da shafin Twitter cikin rudani.

Likitan wanda ya sanya sunansa a shafin Twitter da Dr Maxvayshia, ya bayar da labarin yadda ya fara rashin lafiya, ya san cewa mutuwa zai yi sai ya kira 'yan uwansa domin yayi musu wasiyya a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2017. Ya ce a lokacin da yake bayar da wasiyyar sai yaji an cire mishi ranshi daga jikinshi.

Sannan ya cigaba da bayar da labarin abinda ya faru a lahira a lokacin da ya tsinci kanshi a can.

Haka kuma ya bayyana cewa yadda aka bayyana mishi cewa yanzu lokacin mutuwar shi bai yi ba, hakan yasa aka dawo masa da ranshi gangar jikinshi.

KU KARANTA: Allah Sarki: Mansura Isah ta fashe da kuka yayin da take magana akan irin halin da 'ya'yan talakawa ke ciki

Da ya dawo duniya ya bayyana cewa ya mutu na tsawon mintuna 45 ne, hakan yasa dole ya nemi maganin mutuwar kwakwalwa na wani dan lokaci. Ya kara da cewa kuma dole sai ya kara sabon karantar mutane da sunayensu.

Ya fara bayar da labarin nashi kamar haka: "Naga abubuwa da yawa da mutanen duniyar nan baza su so jin labarinsu ba, baza ma su yarda ba. Amma duk ana yaudarar mu da addini, kuma da yawa baza su taba ganewa ba har sai sun mutu."

Ya kara da cewa "Duk wanda ya ce muku babu rayuwa bayan mutuwa tabbas yana yaudarar kune, ya kamata ku sani tun yanzu kafin lokaci ya kure muku."

Mutane sun shiga rudani da wannan labari na mutumin inda wasu suke ganin karya yake yi. Wasu kuma suka ce su suna so su san ko cewa akwai wutar Jahannama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel