Daliban Kaduna za su daina amfani da takarda da biro wajen zana jarabawa

Daliban Kaduna za su daina amfani da takarda da biro wajen zana jarabawa

Gwamnatin jahar Kaduna a karkashin jagorancin Malam Nasir Ahmad El-Rufai ta bayyana cewa ta fara shirye shiryen kawar da tsarin rubuta jarabawa da takarda da biro domin rungumar tsarin kimiyya da fasaha wajen amfani da na’urar kwamfuta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a garin Kaduna inda yace sun shiga hadin gwiwa da wata kamfanin kimiyya da fasaha, Derusa Nigeria Enterprises Consultancy Services wajen tabbatar da wannan manufa.

KU KARANTA: IRT sun kama gagararren jagoran yan bindiga da ya sace mutane 50 a Kaduna

Babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi ta jahar Kaduna, Phoebi Yayi wanda ta wakilci gwamnan a taron kwanaki 3 inda aka horas da malaman sakandarin jahar a kan yadda ake zana jarabawa a kwamfuta domin su san yadda zasu gudanar da jarabawar a kan daliban.

“Nan gaba kadan zamu kawar da jarabawar takarda da biro a makarantun gwamnati, tare da rungumar jarabawar kwamfuta, saboda idan bamu yi ba dalibanmu zasu yi asara, don haka a yanzu haka mun fara shirye shiryen aiwatar da hakan.

“Amma hakan ba zai yiwu ba idan har Malaman basu samu wannan ilimi ba, saboda da shi ne za su koyar da daliban yadda zasu yi amfani da kwamfuta wajen yin karatu tare da zana jarabawar.” Inji shi.

Da yake nasa jawabi, shugaban kamfanin Derusa, ya bayyana cewa manhajar da suka kirkira ta EasiPREP CBT tana baiwa dalibai daman su shirya ma kansu jarabawar gwaji domin shirya kansu ga babban jarabawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel